Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-13 15:55:37    
Kasar Sin za ta gabatar da sabuwar jarrabawar HSK

cri

A shekarar da muke ciki, kasar Sin za ta gabatar da wata sabuwar jarrabawa don jarraba Sinanci da mutanen kasashen waje suke iya magana da shi a fannin yin cinikayya tsakanin kasa da kasa. A ran 24 ga watan Oktoba, an riga an amince da mutane da suka yi ragista domin shiga jarrabawar. To, a cikin shirinmu na yau, za mu yi muku bayani kan wannan sabuwar jarrabawa.

A da, kasar Sin ta shirya wata jarrabawa domin jarraba Sinanci da mutanen kasashen waje suke iyawa, wadda ake kiranta HSK a takaice. Ya zuwa shekarar da ta gabata, yawan mutanen da suka shiga irin wannan jarrabawa ya kai kusan dubu 500. Yanzu za a gabatar da wata sabuwar jarrabawa wadda ake kiranta C.TEST a takaice, ta yadda za a iya tabbatar da matsayin mutanen kasashen waje wajen yin amfani da Sinanci a cikin zaman yau da kullum.

Furofesa Sun Dejin, shugaban cibiyar jarrabawar Sinanci ta jami'ar harsuna ta birnin Beijing ya bayyana cewa, cibiyar da yake ciki ita ce za ta gabatar da wannan sabuwar jarrabawa. Kuma muhimmin bambanci da ke tsakanin jarrabawar C.TEST da ta HSK shi ne C.TEST ta fi mai da hankali kan jarraba Sinanci da mutanen kasashen waje da suke iyawa a fannin kasuwanci da cinikayya tsakanin kasa da kasa. Kuma ya gaya mana cewa,

"Jarrabawar HSK ta fi mai da hankali a kan jarraba Sinanci da mutanen kasashen waje da ke shiga jarrabawar suke iya yin amfani da shi a fannin nazarin ilmin Sinanci da kuma yin amfani da shi a zaman rayuwarsu. Amma mutanen kasashen waje masu dimbin yawa da ke koyon Sinanci suna da bukatunsu daban, wato suna son yin amfani da Sinanci yayin da suke yin cinikayya, sabo da haka cibiyarmu ta shirya wannan jarrabawa."

Haka kuma furofesa Sun ya bayyana cewa, a cikin tambayoyin da ke cikin jarrabawar C. TEST, ana dora muhimmanci kan jarraba Sinanci da mutanen kasashen waje suke iyawa lokacin da suke yin amfani da shi a cikin zaman rayuwarsu da kuma aikinsu, sabo da haka jarrabawar za ta shafi kalmomin Sinanci masu yawa da za a yi amfani da su a cikin harkokin cinikayya. A waje daya kuma ana mai da hankali kan jarraba Sinanci da mutanen kasashen waje suke iyawa a fannin gwajin murya.

Wannan sabuwar jarrabawa ta kasu matakai iri biyu, wato mataki na farko da na biyu. Idan mutanen waje suka koyi Sinanci har awoyi 200, to za su iya shiga jarrabawar C.TEST ta mataki na farko. Kuma idan suka koyi Sinanci a kasar Sin har shekaru biyu ko uku, to za su iya shiga jarrabawar ta mataki na biyu.

Ban da wannan kuma furofesa Sun ya ce, a shekarar da muke ciki, za a gudanar da wannan jarrabawa a kasashen Sin da Japan a ran 19 ga wata. Daga baya kuma kasar Sin za ta ci gaba da yada jarrabawar zuwa kasar Korea ta Kudu da sauran kasashe. Haka kuma za ta bayar da tambayoyin da ke cikin C.TEST a fili bayan da aka kammala jarrabawar, ta yadda mutane masu neman shiga jarrabawar za su iya share fage.

A ran 24 ga watan Oktoba, an riga an amince da mutane da suka yi rajista domin shiga jarrabawar C.TEST, amma mutane kadan ne suka je jami'ar harsuna ta Beijing don yin rajistar shiga jarrabawar. Game da wannan, furofesa Sun bai nuna damuwa sosai ba. Ya gaya mana cewa,

"bisa matsayinta na wata sabuwar jarrabawa, sannu a hankali za a karbi C.TEST. A ganina, kamfanoni da hukumomi da ke kasar Sin da kasashen waje za su karbe ta a nan gaba, kuma za su mai da ta tamkar wani ma'aunin jarraba kwarewar aikin ma'aikatansu."

Kuriyama Satoshi, wani dalibin kasar Japan da ke koyon Sinanci a jami'ar harsuna ta Beijing ya gaya wa wakilinmu cewa, ya fi son wannan sabuwar jarrabawa da ake kiranta C.TEST idan an kwatanta ta da jarrabwar HSK. Kuma ya ce,

"A ganina, abubuwa masu yawa da ke cikin jarrabawar HSK ba safai mu kan yi amfani da su a cikin zaman rayuwarmu ba. Amma sabo da wannan sabuwar jarrabawa ta shafi abubuwa masu yawa game da kasuwanci da cinikayya, shi ya sa tana da amfani sosai, kuma za ta ba da taimako ga mutanen kasashen waje da suke niyyar gudanar da ayyukansu a kamfanonin kasar Sin. Bugu da kari kuma, mutanen kasashen waje da yawa da ke koyon Sinanci ba su san kalmomin Sinanci sosai ba, amma idan suka saurari maganganun Sinanci, to za su iya ganewa sosai. Shi ya da idan sabuwar jarrabwa ta mai da hankali a kan gwajin muryar mutanen kasashen waje, to ya fi kyau gare su. Dalilin da ya sa na fadi haka shi ne jarrabawar HSK ta fi dora muhimmanci kan jarraba Sinanci da mutanen kasashen waje suke iyawa a fannin kalmomi da nahawun Sinanci. "(Kande Gao)