Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-13 15:53:19    
Kabilar Dongxiang

cri

Kabilar Dongxiang, an samu wannan suna ne sabo da 'yan kabilar ke da zama a yankin Dongxiang na jihar Gansu ta kasar Sin. Kafin kafuwar kasar Sin a cikin shekara ta 1949, an taba kiran kabilar da suna "kabilar Hui ta yankin Dongxiang " da "kabilar Mongolia ta yankin Dongxiang". Yanzu ana fi samun 'yan kabilar a cikin gundumar kabilar Dongxiang mai cin gashin kai da ke yankin Linxia ta kabilar Hui mai cin gashin kai. Bisa kidayar yawan mutanen kasar Sin a karo na biyar da aka yi a cikin shekara ta 2000, yawan 'yan kabilar Dongxiang ya kai dubu 500. 'Yan kabilar suna yin amfani da harshen Dongxiang, kuma yawancinsu suna iya sinanci. Amma 'yan kabilar Dongxiang ba su da harafinsu ba, suna yin amfani da harafin sinanci.

Yankin Dongxiang inda yawancin 'yan kabilar ke da zama yana kan tuddai, sabo da haka ne sharadin yanayi wajen aikin noma ba ya da kyau, kuma halin zaizayar kasa da ake ciki yana da tsanani sosai, ko kusa gonaki ba su fitar da amfanin gona ba. Bayan da aka 'yantar da kasar Sin, sabo da taimakon da Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin da gwamnatocin wurare daban daban na kasar suka bayar, 'yan kabilar Dongxiang sun yi matukar kokari don kyautata halin fama da talauci da kabilar ke ciki. An raya ayyukan ba ruwa da dasa bishiyoyi, sabo da haka ne an kyautata matsalar hasarar amfanin gona sakamakon zaizayar kasa, kuma yawan amfanin gona yana ta samu karuwa. Ban da wannan kuma an gina hanyoyin motoci da yawa, motoci ya iya isa kusan dukkan kauyukan yankin nan.

'Yan kabilar Dongxiang suna bin addinin Musulunci. Sabo da haka, su kan yi wanka. Ba su ci naman gabas da na dakawi da na kore, kuma ba su sha jinin dabbobi.(Kande)