Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-10 19:54:19    
Ba a sami sauye-sauyen kwayoyin cutar murar tsuntsaye a kudancin kasar Sin ba

cri
Ran 10 ga wata, a nan Beijing, a gun taron mamena labaru da aka yi, jami'an aikin noma na kasar Sin kuma masana masu ilmin shawo kan cutar murar tsuntsaye na kasar sun bayyana cewa, ba a samu sauye-sauyen kwayoyin cutar murar tsuntsaye a kudancin kasar Sin ba, labarin da kasashen waje suka bayar na wai an samu sauye-sauyen kwayoyin cutar murar tsuntsaye a kudancin kasar Sin ba shi da kan gado. Sun kuma kara da cewa, matakan da kasar Sin ke dauka wajen shawo kan irin wannan cutar a yanzu suna aiki yadda ya kamata, kasar Sin ta kuma kara yin hadin gwiwa da Kungiyar Kiwon Lafiyar Dabbobi ta Duniya wato OIE da sauran hukumomin duniya.

A kwanan baya, mujallar PNAS ta kasar Amurka ta ba da labarin cewa, an samu sauye-sauyen kwayoyin cutar murar tsuntsaye a kudancin kasar Sin, kuma irin wadannan kwayoyi sun kama tsuntsaye a kasashen Laos da Malaysia da Thailand, mai yiwuwa ne za su yadu a Kudu maso Gabashin Asiya har ma a duk babban yankin Turai da Asiya a karo na 3.

A gun taron manema labaru da aka yi a yau a nan Beijing, shugaban hukumar lafiyar dabbobi ta ma'aikatar aikin gona ta kasar Sin Jia Youling ya karyata labarin da mujallar Amurka ta bayar, ya ce,'A gaskiya kuma, ko kusa ba a sami sabbin kwayoyin cutar murar tsuntsaye ba. Bayanan da aka yi a cikin wannan labari na wai cutar murar tsuntsaye ta yadu zuwa kasashen Kudu maso Gabashin Asiya daga kasarmu, kuma wannan mummunar cuta za ta yadu a duk duniya a karo na 3, ba su da kan gado ko kadan. Marubucin wannan labari bai yi amfani da bayanai na gaskiya ba, bai yi nazari ta hanyar kimiyya ba, shi ya sa hasashen da ya yi ba ya da kan gado. Hukumar Abinci da Aikin Gona ta Majalisar Dinkin Duniya wato FAO da Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya wato WHO suna tsayawa kan ra'ayin da kasar Sin ke tsayawa a kai.'

Ban da wannan kuma, mujallar Amurka ta bayyana cewa, allurar rigakafin da kasar Sin take yin amfani da ita domin cutar murar tsuntsaye ba ta shawo kan kwayoyin cuta da ke yaduwa a kudancin kasar yadda ya kamata ba. Gema da wannan kuma, darektar dakin gwaje-gwaje domin cutar murar tsuntsaye na kasar Sin madam Chen Hualan ta bayyana cewa,'Bayan da muka sami kwayoyoin cutar da aka samu a lokuta daban daban kuma a wurare daban daban na kasar Sin, da farko, dakin gwaje-gwajenmu mun yi wa dabbobi allurar rigakafi da muke yin amfani da ita a yanzu, daga baya, mun raba kananan kwayoyin cuta, mu kai musu hari don ganin cewa, ko allurar rigakafin ta iya samar da isasshen kiyayewa ko a'a. Adadin da muka samu ya nuna cewa, allurar rigakafin da muke yin amfani da ita ta iya shawo kan cutar murar tsuntsaye da ke yaduwa a tsakanin tsuntsaye a kudancin kasar Sin yadda ya kamata, har da kashi 100 cikin dari.'

Sa'an nan kuma Mr. Jia ya yi bayanin cewa, yanzu yawan tsuntsayen gida da aka yi musu allurar rigakafi a kasar Sin ya wuce kashi 95 cikin dari, kasar Sin ta shawo kan cutar murar tsuntsaye yadda ya kamata a sakamkon samar da tsare-tsaren kai rahoto da kuma sa ido kan barkewar cutar a tsakanin dabbobi.

Ya kuma yi karin haske cewa,'Bisa bukatar kungiyar OIE, kasarmu ta kai mata rahoto kan barkewar cutar murar tsuntsaye cikin lokaci, a sa'i daya kuma ta kai rahoto ga kungiyoyin FAO da WHO da kuma yankunan Hong Kong da Macao da Taiwan na kasar Sin da kuma kungiyoyin duniya da abin ya shafa, ma iya cewa, kasarmu ba ta jinkirtar da wani abu ba.'

Bugu da kari kuma, kasar Sin tana gabatar da kananan kwayoyin cutar murar tsuntsaye ga kungiyar WHO ba tare da son kai ba.

Mr. Jia ya ce, ma'aikatar aikin gona ta kasar Sin za ta ci gaba da kara hada kanta da kungiyoyin FAO da OIE, a sa'i daya kuma, za ta taimaki ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Sin wajen hada kai da kungiyar WHO cikin himma da kwazo. Ko da yake suna da rashin fahimta kadan a tsakaninsu, amma a galibi dai bangarorin 2 suna hada kansu lami lafiya.(Tasallah)