Aminai makaunatai, da ku da mu, dukanmu mukan jiku kwarai idan muka ga 'yan wasa suka nuna ganinta sosai har suka samu maki mai kyau a gun wasanni na wuce iyaka a taron wasannin Olympic. Amma mutane sukan yi shakka kan gaskiyar bayanai game da yadda wassu 'yan wasa suka kago matsayin bajinta na duniya. Alal misali : a kwanakin baya ba da dadewaba, an haramta shahararren dan wasan gajeren gudu na kasar Amurka wato Mr. Justin Gatlin shiga gasanni har tsawon shekaru 8 saboda ya sha maganin sa kuzari. Mr. Dick Pond, shugaban hukumar yaki da maganin sa kuzari ta kasa da kasa wato WADA ya zo nan Beijing bisa gayyatar da kwamitin wasannin Olympic na kasar Sin ya yi masa, inda ya fadi albarkacin bakinsa game da wannan lamari. Mr. Pond ya saurari rahoto kan aikin da gwamnatin kasar Sin take yi wajen yaki da maganin sa kuzari, ya kuma kai ziyarar gani da ido a ofishin gwaje-gwajen yaki da maganin sa kuzari na kasar Sin, inda ya yi farin ciki matuka da fadi cewa,
' A ganina, kasar Sin ta rigaya ta samu babban ci gaba tun bayan da ta gudanar da yunkurin yaki da maganin sa kuzari. Amma ya kasance da wata doguwar tafiya da za ta bi domin kasar Sin wata babbar kasa ce mai muhimmanci. Na gamsu da ganin yadda ake tafiyar da ayyukan yaki da maganin sa kuzari a nan kamar yadda ya kamata'.
Mr. Pond mai shekaru 64 da haihuwa, shi dan kasar Canada ne. Tun yana saurayi ya taba halarci taron wasannin Olympic na Rome a shekarar 1960, inda ya samu maki mai kyau a fannin wasan iyo. Wannan dai ya bada kyakkyawan tasiri gare shi wajen aikin yaki da maganin sa kuzari da yake yi yanzu. Mr. Pond ya kara da ,cewa lallai taron wasannin Olympic mai girma ne saboda ya samar da kyakkyawar dama ga 'yan wasa wajen yin kokawa tsakaninsu a gu daya bisa matsayin daidaici. Amma abu mai bacin rai shi ne wassu 'yan wasa sun yi magudi da shan maganin sa kuzari. Na ji dadi sosai lokacin da nake halartar taron wasannin Olympic. Ina so in yi matukar kokari gwargwadon iyawa domin sa 'yan wasa na wannan zuri'a su ji dadi kamar yadda na yi a da.
Mr. Pond ya yi aiki a kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa bayan ya yi ritaya. Ya taba zama mataimakin shugaba da kuma mamban zartarwa na kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa; A sa'I daya kuma ya taba zama shugaban kwamitin kula da harkokin watsa labarai ta telebijin da kuma sauran wassu muhimman kwamitoci na kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa. Lallai Mr. Pond ya bada taimako mai kyau ga bunkasa wasannin motsa jiki na Olympic a cikin shekaru 20 zuwa 30 da suka shige. A shekarar 2000, Mr. Pond ya bar mukamin mataimakin shugaban kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa. Daga baya dai, ya sanya duk karfin da yake da shi kan aikin yaki da maganin sa kuzari, ya kuma zama shugaban hukumar yaki da maganin sa kuzari ta duniya wato WADA har zuwa yanzu. Mr. Pond ya ce, dalilin da ya sa ya yi haka ne shi ne domin ya gane cewa maganar shan maganin sa kuzari ta riga ta zama tamkar ciwon daji ne mafi muni dake kawo illa ga wasannin motsa jiki na duniya. Ya jaddada, cewa shan maganin sa kuzari da akan yi a gun wasannin motsa jiki, wata matsanancin magana ce da ake fuskanta. Wajibi ne mu daidaita ta.
A matsayin shugaban hukumar WADA, Mr. Pond yana ganin, cewa manufar gaskiya ta aikinsu ita ce ana fatan kasancewar hukumar yaki da maganin sa kuzari za ta kara karfafa zuciya ga wadancan 'yan wasa wadanda ba su sha maganin sa kuzari ba.
Mr. Pond ya furta, cewa mu kam muna cike da imani wajen yin wannan aikin yaki da maganin sa kuzari. Yanzu gwagwarmayar yaki da maganin sa kuzari tana ta samun ci gaba, kuma mutanen da suka fahimci wannan magana kuma suke kokarin warware ta sai kara yawa suke a kowace rana. Kazalika,mun kara samun fasahohin nazari da kuma dabarun gwaje-gwaje na zamani. Hakan ya ja kunnen wadancan 'yan wasa a yunkurin shan maganin sa kuzari da suke yi cewa ai hali mai tsanani ne suka shiga.
Maganar shan maganin sa kuzari ta fato ne tun tuni. Saboda haka, ba za a yi tsammanin daidaita ta cikin kwana daya ba. Mr. Ponda ya karfafa magana, cewa kara ba da ilmi ga samari matasa a wannan fanni, wata hanya ce daya tak da za a bi wajen daidaita wannan magana. Ya ce, ilmantarwa, amsa ce ta daidaita wannan magana.
Game da taron wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008, tabbatar da ganin wani gagarumin taron wasannin Olympic mai tsabta ta hanyar yin amfani da dabarun duddubawa na zamani da kuma daukar matakin yanke hukunci mai tsanani, wani babban buri ne na gwamnatin birnin Beijing. A karshe dai, Mr. Pond ya yi kira ga 'yan wasa na kasashe daban daban na duniya da su yi shiri kamar yadd ya kamata don shiga wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008, ta yadda za su kara samar da girmamawa ga wasannin Olympic.( Sani Wang )
|