Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-09 21:17:15    
Mutanen Afirka sun yaba wa taron koli na Beijing tsakanin Sin da Afirka

cri

Bayan da aka rufe taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka, kafofin watsa labarai da kwararru da masana na kasashen Tanzania da Cote d'Ivoire da Senegal da sauran kasashe sun buga labarai da kuma yin jabawai, inda suka nuna yabo ga kasar Sin cewa, kasar Sin kasa ce da take iya shan wahaloli tare da kasashen Afirka, kuma ita sahihiyar aminiya ce ta Afirka.


Jaridar Guardian ta kasar Tanzania ta bayyana cewa, sabo da kasar Sin ta samar da taimako ga kasashen Afirka ba tare da ko wane sharadin siyasa ba, shi ya sa ita sahihiyar aminiya ce ta kasashen Afirka.
Kamfanin dillancin labarai na kasar Cote d'Ivoire ya nuna cewa, kira wannan taron koli ba kawai ta shaida ingantuwar matsayin kasar Sin a duk duniya ba, har ma ta alamanta cewa, dagantakar hadin gwiwa tsakanin Afirka da Sin don moriyar juna ta taka wani sabon mataki.


Kuma masana na jami'ar Dakar ta kasar Senegal sun yi bayani a gaban kafofin watsa labarai cewa, Afirka ba ta yi imani da cewa, kasar Sin tana yin wani sabon mulkin mallaka a Afirka ba. Babban sakamako mai kyau da aka samu a gun taron ya shaida cewa, lalle kasar Sin tana dukufa kan samun zaman lafiya da bunkasuwar Afirka cikin sahihanci, tabbas ne dangantakar hadin kai ta aminci tsakanin Afirka da Sin za ta ci gaba da samun bunkasuwa a cikin sabon halin da ake ciki yanzu.(Kande Gao)