Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-09 15:48:54    
Taro na 1 zuwa na 6 na wakilan Kwamitin tsakiya na 16 na Jam'iyyar Kwaminisanci ta kasar Sin

cri

A ran 11 ga watan Oktoba , an rufe taro na 6 na dukkan wakilai na Kwamitin Tsakiya na 16 na Jam'iyyar kwaminisanci ta kasar Sin wanda aka shafe kwanaki 4 ana yin sa a nan birnin Beijing. Taron ya tatauna kuma ya zartas da " Kudurin da Kwamitin tsakiya na JKS ya tsayar kan wasu manyan matsaloli game da raya zaman al'umma mai jituwa ta kasar gurguzu" , kuma an tsai da manyan makasudai 9 da za a tabbatar da su zuwa shekarar 2020 , ciki har da kyautata tsarin dokokin shari'a da rage bambamcin dake tsakanin birane da kauyuka kuma tsakanin shiyyoyi daban daban . Me ya sa yanzu kasar Sin ta gabatar da maganar raya zaman al'umma mai jituwa ? Me Ya sa aka mai da wannan magana bisa matsayin wata sanarwa na tsarin ka'ida? To , bari mu tabo magana kan wadannan matsalolin .

Tun shekarar 1978 zuwa yanzu , an riga an shafe shekaru 28 ana yin gyare-gyaren tattalin arzikin kasar Sin , kuma an samu manyan nasarorin da suka jawo hankulan kasashen duniya ko a wajen karuwar tattalin arziki ko kuwa a wajen sauyawar tsarinsa . Amma an bullo da wasu sabane-sabane da matsaloli ciki har da yin rabe-rabe ba daidai ba, bambancin da ke tsakanin masu arziki da masu talauci ya karu fiye da kima, da matsalar cin hanci da yin rashawa, da kazamcer muhalli da rishin samun ci gaba wajen ba da ilmi na farko. Wadannan matsalolin sun jawo mugun tasiri ga zaman al'umma mai jituwa kuma cikin kwanciyar hankali, kuma sun yi barazana ga kara bunkasa tattalin arzikin kasar Sin da sauri.

Wadannan matsalolin da suke kasancewa yanzu sun bullo ne bisa dalilai daban-daban wadanda suka zo daga zaman al'umma, sa'an nan kuma sun bayyana cewa, wasu sabani sun bullo a lokacin da ake yin gyare-gyare. Wadannan sabani sun shafi tsarin yankunan kasa na kauyuka, da ikon mallakar masana'antun gwamnatin kasar, da tsarin raba kudade, da tsarin samun tabbacin zaman al'umma, da tsarin buga haraji. Amma raya zaman al'umma mai jituwa yana da ma'ana cewa, gwamnatin kasar Sin za ta kyautata tsare-tsaren da suka shafi zaman rayuwar jama'a wadanda suka shafi kauyuka da samun aikin yi da likitanci da kiyaye muhalli, ta yadda za a rage mugun tasirin da aka jawo a lokacin da ake tafiyar da mulkin kasar.

Yau da shekaru 2 da suka wuce, karo na farko ne kasar Sin ta gabatar da maganar raya zaman al'umma mai jituwa a gun taro na 4 na dukkan wakilai na kwamitin tsakiya na 16 na J.K.S. Mr. Hu Jintao, babban sakataren kwamitin tsakiya na J.K.S. ya gabatar da muhimman halayen musamma 6 ga zaman al'umma mai jituwa wato su ne, tafiyar da tsarin dokokin shari'a cikin dimokuradiyya, a yi kome cikin adalci da gaskiya, amince wa juna, da cike da rayayyen halin aminci, da samun kwanciyar hankali, kuma a yi zaman jituwa tsakanin mutane da halittu.

Cikin kudurin da aka tsayar a gun taro na 6 na dukkan wakilai na kwamitin tsakiya na 16 na J.K.S. da aka yi kwanan baya, an tsai da manufar raya zaman al'umma mai jituwa, wato zuwa shekarar 2020, za a kara kyautata tsarin dokokin shari'a na dimokuradiyya, kuma za a girmama da tabbatar da ikon jama'a. Ban da wannan kuma za a rage bambancin da ke tsakanin birane da garuruwa, kuma tsakanin shiyyoyi daban-daban, da tsara tsarin raba kudade ga jama'a cikin adalci kuma ta tsararriyar hanya, za a daidaita matsalar samun aikin yi sosai, yawan albarkatun kasa da za a aiwatar da su zai karu sosai, muhallin halittu kuma zai samu kyautatuwa a bayyane, ta yadda za a bullo da wani halin mai kyau wato kowa ya yi aiki gwargwadon iyawarsa kuma ya sami lada gwargwadon aikinsa, kuma dukkan jama'a su yi zama tare cikin jituwa.

Muhimman manufofin bunkasa tattalin arziki da zaman al'umma

"Tsarin ka'idoji na shiri na 11 na shekaru 5-5 na raya tattalin arzikin kasa da zaman al'umma" na kasar Sin ya gabatar da muhimman manufofin bunkasa tattalin arziki da zaman al'umma cikin shekaru 5 masu zuwa. Bisa babban bukatun da aka yi wajen raya zaman al'umma mai wadata daga duk fannoni, muhimman manufofin bunkasa tattalin arziki da zaman al'umma da za a yi kokarin tabbatar da su a lokacin "shiri na 11 na shekaru 5-5".(Ado)