Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-08 19:39:24    
Sabuwar huldar abokantaka da ke tsakanin Sin da Afirka bisa manyan tsare-tsare hulda ce mai muhimmanci

cri

Tun bayan da sabuwar kasar Sin da kasashen Afirka suka kulla huldar diplomasiyya a tsakaninsu yau da shekaru 50 da suka wuce, jama'ar Sin da Afirka sun hada kansu, su goyi bayan juna, su tsaya tsayin daka kan ka'idoji da ra'ayoyi na yin mu'amala cikin sahihanci da yin zaman daidai wa daida da moriyar juna da kuma hada kai da hada gwiwa don samun bunkasuwa tare, sun rika zurfafa zumunci a tsakaninsu, shi ya sa suka sami sakamako mai yawa.

Kasashen Sin da Afirka sun tanadi abubuwa da yawa a cikin tsarin dandalin hadin gwiwa da kuma matakai da manufofin da suke dauka, ta haka sun kawo wa jama'arsu alheri sosai.

Bayan da aka kafa dandalin, an ci nasarar kiran tarurukan ministoci sau 3 da wani taron koli, dandalin hadin gwiwa tsakanin Sin da Afika ya zama muhimmin dandali da tsari ne mai amfani wajen yin tattaunawa tsakanin bangarori daban daban, da yin mu'amalar fasahohin zamani na tafiyar da kasa da harkokin siyasa, da karfafa amincewa da juna, da kuma yin hadin gwiwa yadda ya kamata. Takardun da aka zartas da su a jere a gun dandalin a cikin shekaru 6 da suka shige sun jagoranci Sin da Afirka wajen kyautata hadin gwiwa da kuma samun ci gaba. A sa'i daya kuma, kasar Sin ta goyi bayan sa kaimi kan shirye-shiryen ayyuka na dandalin da 'sabon shirin abokai kan bunkasa Afirka' da kuma shirye-shirye na kasashen Afirka kan bunkasa zaman al'ummar kasa da tattalin arziki domin taimakon juna da hada kai.


1  2  3