Don murnar kiran taron dandalin tattaunawa kan hadin guiwar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika a birnin Beijing, sai a ranar 25 ga watan Oktoba , kungiyoyin wasannin fasahohi da 'yan wasannin fasaha da suka zo daga kasashen Masar da Afrika ta kudu da sauransu guda uku sun shirya shagalin dare na musamman da ke da lakabi haka: "Daren Afrika" a nan birnin Beijing. Gidan baje koli na kasar Sin shi ma ya shirya wani nunin nagartattun kayayyakin fasahohi na kasashen Afrika. Tun daga ranar da ta cika shekaru 50 da kulla huldar diplomaisya a tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika har zuwa yanzu, kasar Sin da kasashen Afrika suna ta kara tsawaitawa da samun bunkasuwa wajen yin ma'amalar al'adu, a cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, ma'amalar nan sai kara yawa suke yi, ta kara wa jama'ar Afrika da Sin fahimcin juna da zumunci .
Abin da kuke saurara shi ne wasannin kade-kade da wake-wake na Afrika ta Kudu da aka yi, wato kungiyar 'yan wasannin fasaha ta Umkhonto na kasar Afrika ta kudu tana nan tana nuna wasannin kwaikwayo da ke da lakabi haka: kyakkyawan al'adu. 'yan wasanni na kasar Afrika ta Kudu sun bayyana al'adun kasarsu da ke da halaye iri daban daban ta hanyar wake-wake da kade-kade da kuma raye-raye iri iri da yawa. 'Yan wasa sun burge kowane dan kallon wasanninsu ta hanyar nuna fasahohinsu cikin himma da kwazo tare da 'yanci sosai. Bayan kammalar nuna wasannin, manema labaru sun ziyarci wasu 'yan kallon kasar Sin. Wata 'yar kallo ta bayyana cewa,
a ganina, wasannin da suke nuna daga zuciyarsu ne, suna da karfin ba da tasiri sosai ga mutane, da wuya a kan iya samun damar kallon irin wasannin da suka yi a kasarmu, sun jawo sha'awata da hankalina sosai. Na ji karfin rayuwa na gaskiya a karo na farko, a gaskiya dai suna da kyau sosai.(Halima)
|