Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-08 15:36:08    
Yadda kasar Sin take a idon masu sauraronmu(3)

cri

Kwanan nan, mun gabatar da wani bincike a tsakanin masu sauraronmu dangane da 'me ka sani game da kasar Sin', kuma nan da nan ba da dadewa ba, mun sami amsoshi da yawa daga masu sauraronmu, inda suka fadi duk abubuwan da suka sani game da kasar Sin, kuma gaskiya masaniyar da masu sauraronmu suke da ita dangane da kasar Sin ta burge mu kwarai.

Malam Nura Abdullahi daga birnin Kano na kasar Nijeriya ya rubuto mana cewa, abin da na sani game da kasar Sin shi ne, kasar Sin kasa ce dake cikin yankin Asiya kuma kasar Sin tana da yawan al'umma da kuma kabilu iri daban daban da kuma addinai iri daban daban, kuma na san mutanen kasar Sin mutane ne masu kishin kasarsu da kuma kishin kansu. Bayan haka, na sani mutanen Sin ba masu zaman banza ba ne, suna da kishin neman abin kansu a wajen neman ilmi ko kasuwanci da ci gaban kasar Sin. kasar Sin ta shahara a wajen kere-kere da ilmin zama da tattalin arziki. Bayan haka, Sin ta shahara a duk duniya a fannoni daban daban da suka hada da na kasuwanci da taimakon kasashe masu tasowa da kuma kasancewar Sin mai kujerar dindindin a majalisar dinkin duniya.

Bayan haka kuma, malami Yusuf ya aiko mana Email, inda ya ce, Sin kasa ce mai mutumci a tsakanin kasashen duniya, ta kare mutuncinta, ba ta yarda da mallakar yammaci ba, tana bayan mulki irin na gaskiya da gar gar. A ko da yaushe muna farin cikin mu ji an ce Sin kawai sai mu ji dadin rayuwa. Tattalin arzikin kasarsu yana ta karuwa musamman yadda arewacin Nijeriya suka kulla huldar cinikayyar haja da su, mutum zai iya kulla ciniki ya je kuma da kansa ya dauko kayansa ba wani shamaki a tsakani, farin ciki da walwala ya samu a tsakani ta yarda mutum zai bugi kirji ya je har Sin ya kulla harkar cinikayya, madallah da wannan kasa. Cinikinsu kullum bunkasa yake, sabo da gaskiyarsu da rikon amana.

Sai kuma malam Sanusi Isah daga birnin Keffi na jihar Nasarawa ta kasar Nijeriya ya rubuto mana cewa, kasar Sin wata kasa ce mai tasowa tare da bunkasar tattalin arziki cikin sauri, kuma tana yin hulda da kasashen duniya daban daban. kamar kasa ta Nijeriya, kasar Sin tana hulda ta kasuwanci wanda har ya kai duk inda ka shiga a manya manyan kasuwanni na Nijeriya, to, ba za ka iya kirga kayayyakin kasar Sin ba, haka ma a kasashen duniya daban daban. Bayan haka, kasar Sin mamba ce a kungiyar kasuwanci ta duniya da kungiyoyi ta kasuwanci daban daban.

Idan kuma muka koma harkar siyasar duniya nan ma, kasar Sin ba a bar ta baya ba, kasa ce ta daya daga cikin kasashe masu fada a ji a duniya kuma ga shi tana da kujerar na hawan naki a M.D.D. tare da shiga sulhu a duk lokacin da wani matsala ta taso. Wani abu daya da Sin ta shahara shi ne ba ta katsalandan, wato shiga harkokin cikin gida na wata kasa.

Bayan haka kasar Sin tana fama da wadansu matsaloli wadanda basu taka kara suka karyaba kamar siyasa tsakanin Sin da kasar Japan a kan ziyarar da wadansu shugabanni na kasar Japan suka kai ziyara makabarta ta Yasukuni wanda bai dace ba saboda wadannan sojoji na kasar Japan da suka mutu kuma aka rufe su a wannan makabarta sun tabka babban laifi da cin zalin ga Sinawa. Sai kuma maganar yankin Taiwan kowa ya sani cewa yankin Taiwan wani bangare ne na kasar Sin kuma har abada gwamnatin kasar Sin ba za ta amince da 'yancin Taiwan duk kasar da ta shiga cikin wannan magana to hakikan gaskiya ta yi shishigi a harkokin cikin gidan kasar sin.

kamar sauran kasashe na duniya masu al'adu da addinai daban daban, ka ga akwai kabilu sama da hamsin a kasar Sin, sannan kuma ko wace kabila tana da nata al'ada iri daban daban, kuma kasar Sin tana da addinai iri daban daban kamar Musunluci da Buddhist da dai sauran su.(Lubabatu)