Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-08 11:07:53    
Wani kamfanin kasar Sin ya daddale wata kwangilar da kudinta ya kai dallar Amurka miliyan 220 da Zambia

cri
A ran 7 ga wata a nan birnin Beijing, kamfanin hakar bakin karfe na kasar Sin ya daddale wata kwangilar hadin gwiwar da kudinta ya kai dallar Amurka miliyan 220 da gwamnatin Zambia, kuma shugaban kasar Zambia, Levy Patrick Mwanawasa ya halarci bikin daddale kwangilar.

Bisa takardar bayani da bangarorin biyu suka daddale dangane da hadin gwiwar, kamfanin hakar bakin karfe na kasar Sin zai zuba kudin Amurka dalla miliyan 220 don kafa wata masana'antar narke danyen tagulla a kasar Zambia.

Ministan harkokin waje na Zambia, Mundia Sikatana, wanda ya daddale kwangilar a madadin gwamnatin Zambia, ya ce, gwamnatin Zambia tana lale marhabin da masana'antun kasar Sin da su zuba jari a kasar, kuma tana imani da cewa, zambia za ta ci gajiyar hadin gwiar tattalin arziki da ciniki da ke tsakanin bangarorin biyu wanda kuma ke dinga habaka.(Lubabatu)