Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-08 10:58:16    
Mun taba koyar da wasanni a kasashen Afirka

cri
Shekarar bana wato shekarar da muke ciki cikon shekaru hamsin ne da aka fara kulla huldar diplomasiya tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka.Tun bayan shekaru hamsin da suka shige,kasar Sin da kasashen Afirka daban daban suna yin hadin gwiwa sosai a fannin tattalin arziki da na ba da ilmi da na kiwon lafiya da na wasannin motsa jiki da sauransu.Musamman hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka wajen wasannin motsa jiki ya ba da babbar gudumuwa ga bunkasuwar sha`anin wasannin motsa jiki na duniya da zurfafuwar zumunta tsakanin kasashen duniya.Don kara karfafa irin wannan hadin gwiwa,gwamnatin kasar Sin ta taba aika malaman wasa da yawan gaske ga kasashen Afirka,wadannan malamam wasa sun tafi kasashen Afirka kuma sun koyar da wasanni iri daban daban a can,a cikin shirinmu na yau,za mu yi muku bayani kan wannan.

Malama Wu Haojin ita ce wata malamar koyar da wasan tsalle-tsalle da lankwashe-lankwashe a kasar Sin,yanzu tana da shekaru 61 da haihuwa,daga shekara ta 1982 zuwa shekara ta 1984,ta je kasar Morroco domin koyar da wasan tsalle-tsalle da lankwashe-lankwashe a cikin kungiyar wasan tsalle-tsalle da lankwashe-lankwashe ta mata ta kasar,ta ce,`Bayan na sauka a kasar,wato a shekara ta 1982,akwai `yan wasa wajen goma ne kawai,daga baya kuma sun karu,amma ba su wuce ashirin ba,kodayake `yan wasan kasar ba su iya wasan sosai ba wato matsayin wasansu bai kai na gaba ba,amma duk da haka sun shiga gasa,wannan shi ne karo na farko a tarihinsu,shi ya sa kungiyar wasan tsalle-tsalle da lankwashe-lankwashe ta kasar Morroco ta yi farin ciki kwarai da gaske.`

A halin da ake ciki yanzu,cudanya da hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka wajen wasannin motsa jiki suna kara karfafuwa.Tun bayan shekara ta 2000,gaba daya kasar Sin ta aika malaman wasa 38 na wasanni 13 ga kasashen Afirka 12 kamarsu kasar Masar da kasar Habasha da kasar Namibiya.Yanzu dai ana ci gaba da aika malaman wasa ga kasar Ghana da kasar Sudan da kasar Tanzaniya da kasar Nijer da sauransu.

Malam Lu Jianmin shi ne malamin koyar da wasan karate na jami`ar koyar da wasannin motsa jiki ta Beijing,daga shekara ta 1997 zuwa shekara ta 2001,ya tafi kasar Masar don koyar da wasan karate a cikin kungiyar wasan karate ta kasar Masar,ya ce,`A wancen lokaci,na zama malamin wasan karate daya kadai a kungiyar,na sha aiki sosai,amma `yan wasan karate na kasar Masar sun yi kokari,wasan karate ya sami ci gaba a kasar Masar bayan kokarin da muka yi tare.`

A cikin shekaru 50 da suka shige,sau tarin yawa ne kungiyar wasan kwallon tebur da kungiyar wasan tsalle-tsalle da lankwashe-lankwashe ta kasar Sin sun kai ziyara a kasashen Afirka,malaman wasa da yawan gaske sun ba da taimako ga dada daguwar matsayin wasanni na kasar Masar da kasar Nijeriya da kasar Ghana da sauran kasashe.

Ko shakka babu malaman wasa sun fuskanci wahalhalu masu tsanani a kasashen Afirka,alal misali,ba su iya harsunan wuraren kasashen Afirka ba,kuma ba su saba da yanayin can ba,ban da wannan kuma,sharudan cibiyoyin wasannin motsa jiki na can suna kama baya.Amma sun yi kokari kuma sun sami nasara.

Malaman wasa na kasar Sin sun nuna kwazo da himma sun koyar da wasanni a kasashen Afirka,`yan wasa na kasashen Afirka su ma sun yi kokari kuma sun sami sakamako masu kyau a karkashin jagorancin malaman wasa na kasar Sin.a sa`i daya kuma,zumunta tsakaninsu ta kara zurfafuwa a kwana a tashi.Malam Lu Jianmin ya waiwayi cewa,`Na sanin `yan wasan da na koyarwa sosai,mu kan yi hira,kuma su kan kira ni baba yayin da suke yin gasa,muna jin dadi sosai.`

Kodayake ya yi nisa kwarai tsakanin kasar Sin da nahiyar Afirka,amma a cikin `yan shekarun da suka shige,kasar Sin da kasashen Afirka sun warware wahalhalun dake gabansu sun yi aiki da yawa don kara karfafa cudanya da hadin gwiwa tsakaninsu a fannin wasannin motsa jiki.A shekara ta 1986,kwamitin wasannin Olimpic na duniya ya ba da kofin yabo na Olimpic ga kwamitin wasannin Olimpic na kasar Sin don yaba wa kasar Sin saboda kokarin da ta yi wajen ba da taimako wajen wasannin motsa jiki ga kasashe masu tasowa musamman ga kasashen Afirka.(Jamila Zhou)