Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-08 10:56:08    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki(02/11-08/11)

cri
Ran 3 ga wata a birnin Beijing,gwamnatin kasar Sin da gwamnatin kasar Kuwaiti sun daddale kan wata yarjejeniyar hadin gwiwar wasannin motsa jiki tsakanin gwamnatocin kasashen nan biyu.Bisa yarjejeniyar da aka daddale,bangarorin biyu za su sa kaimi ga kungiyoyin wasannin motsa jiki da gwanayen wasannin motsa jiki da `yan kimiyya da fasaha na kasar Sin da kasar Kuwaiti da su kara karfafa cudanya da hadin gwiwa tsakaninsu daga duk fannoni.

Ran 5 ga wata,an kawo karshen gasar yawon kasa kasa ta sana`a ta kungiyar kwallon tebur ta duniya a St.Petersburg.A ran nan,`dan wasa daga kasar Sin Hou Yingchao ya lashe `dan wasa daga kasar Croatia Zoran Primorac ya zama zakaran gasa tsakanin namiji da namiji,kuma ya zama zakaran gasa tsakanin maza biyu biyu tare da wani `dan wasa daban Lin Ju.

Ran 5 ga wata,an yi gasa ta zagaye na karshe tsakanin kungiya kungiya ta gasar cin kofin duniya ta kwallon hannu ta shekara ta 2006 a kasar Japan,kungiyar kasar Rasha ta sami lambawan,kungiyar kasar Jamus ta sami lambatu,kungiyar kasar Sin kuwa ta zama lambatiri.Gaba daya akwai kungiyoyi 24 wadanda suka shiga wannan gasa,kuma za a kammala gasar a ran 16 ga wata.

Ran 5 ga wata,an kawo karshen budaddiyar gasa ta kwallon badminton ta kasar Denmark ta kungiyar kwallon badminton ta duniya wadda aka yi a birnin Aarhus na kasar Denmark,`dan wasa daga kasar Sin Chen Hong ya lashe Chen Yu daga kasar Sin ya zama zakaran gasa tsakanin namiji da namiji,`yar wasa daga kasar Sin Jiang Yanjiao ta lashe Lu Lan daga kasar Sin ta zama zakarar gasa tsakanin mace da mace.

Ran 3 ga wata,an yi gasa ta zagaye na karshe tsakanin kungiya da kungiya ta gasar cin kofin Asiya ta kwallon kafa ta samari wadanda ba su kai shekaru 19 da haihuwa ba a birnin Calcutta na kasar Indya,kungiyar `yan wasa ta kasar Sin ta lashe kungiyar kasar Thailand ta zama zakarar rukunin B kuma ta shiga kungiyoyi 8 masu karfi.Za a kammala gasar a ran 12 ga wata. (Jamila Zhou)