Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-07 21:26:22    
Kafofin watsa labaru na wasu kasashen Afirka sun yaba wa taron koli na Beijing

cri

A 'yan kwanakin baya, bi da bi ne kafofin watsa labaru na wasu kasashen Afirka suka bayar da bayanai ko sharhohi, inda suka yaba wa taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa a kan hadin kai a tsakanin Sin da Afirka, wanda aka rufe ba da dadewa ba.

Kawancen kamfanin dillancin labaru na kasar Kongo(Kinshasa) ya ce, bunkasuwar Afirka za ta sami moriya daga bunkasuwar dangantakar abokantaka da hadin kai a tsakanin Sin da Afirka.

Jaridar 'Sunday Times' ta kasar Afirka ta kudu ta buga maganar kakakin ma'aikakar harkokin waje ta kasar cewa, kasar Sin ta zama wata babbar dama ga Afirka, kasar Sin kuma tana taka wata muhimmiyar rawa wajen sa kaimi ga hadin kai tsakanin kudu da kudu. Kasashen Afirka suna sa ran ganin kasar Sin za ta kara bayar da babban taimako a kan tsare tsaren siyasa da kudi da cinikayya na duniya.

Babbar jarida ta kasar Morocco 'Le Matin' ta bayar da wasikar da sarkin kasar ya rubuta wa taron koli cewa, yanzu lokaci ya yi da za a kara sa kaimi ga hadin kai a tsakanin Sin da Afirka, kasar Morocco za ta yi kokari tare da kasar Sin wajen taimakawa kasashen Afirka da ke kudu da Sahara da kara sa kaimi ga hadin kai a tsakanin Sin da Afirka.

Ban da wadannan kafofin watsa labaru da muka ambata a baya, kafofin watsa labaru na kasashen Yemen da Benin da Angola da dai sauransu su ma suna ganin cewa, taron koli na Beijing zai kara ba da taimako ga dangantakar abokantaka da cinikayya a tsakanin Sin da Afirka.(Danladi)