Kogunan dutse na dutsen Maiji yana kusa da birnin Tianshui da ke lardin Gansu na gabashin kasar Sin. An mayar da dutsen Maiji mai tsayin mita 142 a matsayin dakin nune-nunen mutum-mutumi na gabas. Ma'anar dutsen Maiji a Sinance ita ce dutsen da aka tattara alkama, dalilin da ya sa aka kira shi da wannan suna shi ne saboda siffarsa ta yi kama da wurin da aka tattara alkama.
Akwai kogunan dutse guda 194 a cikin dutsen Maiji, an raba su zuwa kashi 2, wato guda 54 suna gabashin dutsen, sauran 140 suna yammacin dutsen. An saka dukan wadannan kogunan dutse a kan hayi mai tsayin mita misalin 80 daga kasa a kudancin wannan dutse. Kogunan dutse na dutsen Maiji sun hada da mutum-mutumi da aka yi da yumbu ko kuma da duwatsu 7,200 da kuma zane-zanen jikin bango mai fadin murabba'in mita fiye da 1,300.
An samar da wadannan kayayyakin fasaha tun daga karni na 4 zuwa na 19, wato zamanin daular Wei ta Arewa da ta Yamma da Zhou ta Arewa da Sui da Tang da zamanin dauloli 5 na kasar Sin da kuma zamanin daular Song da Yuan da Ming da Qing, shi ya sa kogunan dutse da ke dutsen Maiji suka zama nagartattun misalai ne a fannin sassaka a kasar Sin.
Tsayin mutum-mutumi mafi tsayi a cikin kogunan dutse na dutsen Maiji ya kai misalin mita 16, kuma tsayin wanda mafi karami ya kai misalin santimita 10 kawai.
Mutum-mutumi na yumbu da ke cikin dutsen Maiji sun yi suna ne ba a cikin kasar Sin kawai ba, har ma sun shahara sosai a kasashen ketare. Babban sigar musamman na kogunan dutse na dutsen Maiji shi ne aka shimfida wata hanyar katako kawai a kan hayin dutsen don hada dukan kogunan dutse tare. Manyan kayayyakin da aka samar da su don kiyaye mutane a lokacin da suke tafiya a kan wannan hanyar katako su kan ba masu yawon shakatawa mamaki sosai.
Kungiyar Ilmi da Kimiyya da Al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya wato UNESCO ta tanadi kogunan dutse na dutsen Maiji a cikin takardar sunayen wuraren tarihi na duniya.(Tasallah)
|