Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-07 15:59:55    
Firaministan kasar Sin ya gana da wasu shugabannin kasashen Afirka

cri
A ran 6 ga wata a nan birnin Beijing, bi da bi ne firaministan kasar Sin, Wen Jiabao ya gana da shugaban kasar Afirka ta kudu, Thabo Mbeki da shugaban kasar Masar, Mohammed Hosni Mubarak, da dai sauran wasu shugabannin kasashen Afirka.

A yayin da yake ganawa da Mr.Mbeki, Mr.Wen ya jaddada cewa, inganta zaman lafiya da bunkasuwar Afirka da karfafa hadin gwiwar aminci a tsakanin Sin da Afirka manufa ce ta gwamnatin kasar Sin. Bangaren Sin zai kara inganta huldar kawance da ke tsakaninta da kasashen Afirka, kuma za ta yi kokarin goyon bayan sabon shirin abokai na Afirka, wato NEPAD, kuma za ta yi kira ga gamayyar kasa da kasa da su kara kulawa da moriyar kasashen Afirka, su kara ba su taimako.

Mr.Mbeki ya ce, Afirka ta kudu da sauran kasashen Afirka sun taya murnar taron koli na dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka, kuma sun nuna yabo kwarai a kan taimakon da kasar Sin ke bayarwa ga kasashen Afirka cikin sahihanci.

A yayin da yake ganawa da shugaba Mubarak kuma, Mr.Wen ya yi fatan kasashen Sin da Masar za su kara daidaitawa a tsakaninsu, su ingiza hadin gwiwa a tsakanin kasashe masu tasowa da kuma shawarwari a tsakanin kasashe masu tasowa da kasashe masu ci gaba. Mr.Wen ya kuma kara da cewa, kasar Sin tana son kara hadin gwiwa da Masar, su sa kaimi ga bangarori daban daban da abin ya shafa da su bi hanyar shawarwarin siyasa don daidaita matsalolin Gabas ta takiya, ciki har da matsalar Palasdinu da Isra'ila daga dukan fannoni, kuma cikin adalci.

Mr.Mubarak ya kuma yaba wa rawa mai yakini da kasar Sin ke takawa wajen ingiza aikin shimfida zaman lafiya a gabas ta tsakiya.(Lubabatu)