Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-07 15:43:43    
Duniya na lura da yadda za ta taimaka wa Afrika wajen magance sauye-sauyen yanayi

cri
Ran 6 ga wata, an bude gagarumin taron majalisar dinkin duniya kan sauye-sauyen yanayi na shekarar 2006 a zauren hukumar tsare-tsaren muhalli ta majalisar dinkin duniya da ke a birnin Nairobi, hedkwatar kasar Kenya. Wakilai sama da 6000 wadanda suka fito daga kasashe sama da 160 da jami'an majalisar dinkin duniya sun halarci taron. A lokacin taron, za a yi tarurrukan kasa da kasa da dama a kan batutuwan yanayin duniya, daga cikinsu akwai taro na karo na 12 na bangarori da suka cimma "yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya kan sauye-sauyen yanayi", da taro na karo na 2 na bangarori da suka daddale "yarjejeniyar Kyoto" da dai sauransu.

Mr Kivutha Kibwana, shugaban taron kuma ministan kare muhalli na kasar Kenya wanda ke shugabantar taron ya yi jawabi a gun bikin bude taron cewa, dumamar yanayi a duniya tana kawo tasiri ga cim ma manufar raya zamantakewar al'umma domin wadanda suka fi fama da talauci a Afrika. Sabo da haka ya yi kira ga duk bangarorin da suka daddale yarjejeniyoyin da su dauki matakai wajen magance sauye-sauyen yanayi. Ya ce, "ko da yake nauyin da ke wuyan ko wace kasa ya sha banban, amma duk da haka ko kasashe masu sukuni ko kuma kasashe masu tasowa gaba daya suna da moriya iri daya wajen magance lahani da suke samu daga sauye-sauyen yanayi. Don haka muna bukatar alkawari da za mu dauka tare, wato mu dauki alkawarin nan bisa halin da ake ciki a kasashe daban daban, kuma bisa tushen daidaici da manufa daya."

Dangane da batun sauye-sauyen yanayi a duniya, bi da bi gamayyar kasa da kasa ta zartas da "yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya kan sauye-sauyen yanayi" da "yarjejeniyar Kyoto". Bisa "yarjejeniyar Kyoto" da aka fara aiki da ita a watan Febrairu na shekarar bara, an nemi kasashen masana'antu 36 da su rage kashi 5 cikin dari na iska maras kyau da sauran irinsu da suke fitarwa a tsakanin shekarar 2008 zuwa ta 2012. Bayan haka kuma za su kara rage yawan iskar maras kyau da sauran irinsu da suke fitarwa.

Da Malam Su Wei, mataimakin shugaban ofishin kula da harkokin yarjejeniyoyi na ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ya tabo magana a kan wannan, inda ya bayyana cewa, "manyan batutuwa biyu da za a daidaita a gun taron bangarori da suka daddale "yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya kan sauye-sauyen yanayi" su ne, na farko, a tattauna asusu da za a kafa don ba da taimakon kudi ga kasashen Afrika musamman kasashe mafi talauci ta yadda za su dauki matakai wajen magance sauye-sauyen yanayi, na biyu kuwa, a sa kaimi ga samar da fasaha, dalilin da ya sa haka shi ne domin samun fasaha ta zamani babbar hanya ce daya take da ake bi wajen daidaita batun sauye-sauyen yanayi. Kasashe masu sukuni suna mallakar fasaha ta zamani, kuma su kware wajen binciken fasaha, don haka suna sauke nauyin da ke bisa wuyansu na taimaka wa kasashe masu tasowa wajen daukar matakai don magance sauye-sauyen yanayi."

Malam Achim Steiner, shugaban zartaswa na hukumar tsare-tsaren muhalli ta majalisar dinkin duniya ya ce, ana yin wannan taro a kasar Afrika musamman domin jawo hakulan gamayyar kasa da kasa a kan kalubalen sauye-sauyen yanayi da Afrika ke fuskanta. Ya ce, "nahiyar Afrika nahiya ce da ke fitar da iska mafi kadan da ke dumama yanayi a duniya. Amma tana gamuwa da tasiri mafi tsanani daga sauye-sauyen yanayi a duniya. Ga shi kasashen Afrika ba su iya binciken tasirin da suke samu daga sauye-sauyen yanayi ba. Da ganin haka, muna kokari wajen yin kira ga gamayyar kasa da kasa da su lura da kalubalen sauye-sauyen yanayi da Afrika ke fuskanta, ba ma kawai canja irin wannan hali nauyi ne da kasashen Afrika ke saukewa bisa wuyansu ba, har ma gamayyar kasa da kasa su ma suna sauke da nauyi bisa wuyansu."(Halilu)