
A ran 6 ga wata a birnin Beijing, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya gana da wasu shugabannin Afirka da suka halarci taron koli na dandalin tattaunawa a kan hadin kai a tsakanin Sin da Afirka, wadanda suka hada da shugaban kasar Niger Mamadou Tandja da na Afirka ta kudu Thabo Mbeki da na kasar Aljeriya Abdoulaziz Bouteflika da na kasar Benin Thomas Boni Yayi da na kasar Togo Faure Essozimna GNASSINGBE da na kasar Eritrea Isaias Afwerki da na kasar Zimbabuwei Robert Mugabe.
Mr Hu ya nuna godiya ga wadannan shugabanni da suka halarci taron koli na Beijing, yana fata kasar Sin da kasashen Afirka za su yi kokari tare da sada zumunci ga juna da nuna goyon baya ga juna, kuma za su aiwatar da nasarorin da suka samu a gun taron koli na Beijing domin samar wa jama'a jin dadi da kara bunkasa dangantakarsu.
Wadannan shugabannin kasashe 7 sun taya murna ga kasar Sin da ta shirya taron koli na Beijing cikin nasara, sun yaba wa nasarorin da aka samu a gun taron koli na Beijing, haka kuma sun bayyana cewa, taron koli na Beijing yana da muhimmanci sosai ga bunkasuwar Afirka, wannan ya nuna sahihiyar zuciya ta gwamnatin kasar Sin da jama'arta, sun kuma nuna godiya ga babban taimako da kasar Sin ta bayar ga taron koli na Beijing.(Danladi)
|