
A ran 5 ga wata bayan da aka kawo karshen taron koli dandalin tattaunawa a kan hadin kai a tsakanin Sin da Afirka, shugaban kasar Mali Amadou Toumani Toure ya bayyana cewa, an shirya wannan taron koli cikin nasara sosai.
Shugaba Toure ya nuna yaba wa jawabin da takwaransa na kasar Sin Hu Jintao ya yi a gun bikin rufe wannan taron koli. Ya ce, a cikin wannan jawabi, shugaba Hu ba ma kawai ya gabatar da kokarin da kasar Sin take yi wajen karfafa hadin kai a tsakanin Sin da Afirka da kuma sa kaimi ga bunkasuwar Afirka ba, har ma ya bayar da shawarar da kasar Sin ta yanke domin ci gaba da nuna goyon baya ga bunkasuwar Afirka ba. Mr Toure ya ci gaba da cewa, sanarwar Beijing da sauran shirye shirye da aka zartas a gun taron kolin za su ba da jagoranci sosai ga hadin kansu a nan gaba.(Danladi)
|