Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-06 18:36:28    
Kasashen Sin da Afirka suna fuskantar makoma mai kyau wajen yin hadin gwiwa a tsakaninsu

cri

Ran 4 zuwa ran 5 ga wata, a nan Beijing, an yi taron koli na Beijing na dandalin hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, inda shugabanni ko wakilai na kasashe 48 na Afirka suka jagoranci tawagogi don halartar taron. Wannan taro kasaitaccen biki ne a tarihin dangantakar da ke tsakanin Sin da Afirka. Yawancin kasashen Afirka suna ganin cewa, kasashen Sin da Afirka suna fuskantar makoma mai kyau wajen yin hadin gwiwa a fannonin tattalin arziki da al'adu da sauransu.

Tun bayan da aka kafa dandalin hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka yau da shekaru 6 da suka wuce, bangarorin Sin da Afirka sun sami saurin bunkasuwa wajen yin hadin gwiwa don moriyar juna a fannoni daban daban. Wannan dandali ya zama muhimmin dandali ne wajen yin tattaunawa a tsakanin Sin da Afirka da kuma tsari ne mai amfani wajen yin hadin gwiwa yadda ya kamata a tsakaninsu.

Tun daga shekarar 2000 zuwa shekarar 2005, yawan karuwar kudaden da Sin da Afirka suka samu daga wajen yin ciniki a tsakaninsu a ko wace shekara ya wuce goma. Ministan ciniki da masana'antu na kasar Masar Rashid Mohamoud Rashid yana ganin cewa, kasar Sin na daya daga cikin abokai mafi muhimmanci ga kasar Masar ta fuskar tattalin arziki da ciniki, kasar Masar tana dora muhimmanci kan raya dangantakar da ke tsakaninta da kasar Sin ta fuskar tattalin arziki da ciniki. Ya kamata masana'antun kasashen 2 su kara fahimtar juna, su kara samar da damar yin hadin gwiwa. Ya ce,'A cikin shekarun nan da suka wuce, cinikin da ke tsakanin Sin da Masar yana samun bunkasuwa, muna fatan za mu tabbatar da raya shi zuwa sabon mataki ta hanyar cimma yarjejeniyoyi a jere. Gwamnatocin Sin da Masar dukansu suna dora muhimmanci kan yin hadin gwiwa a tsakanin masana'antu matsakaita da kanana, kulla dangantaka a tsakaninsu yana da muhimmanci sosai. Bangarorin 2 suna fuskantar makoma mai kyau wajen yin hadin gwiwa a fannonin kayayyakin lantarki da na sassaka da aikin hadar magunguna da dai sauransu.'

A sa'i daya kuma, kasar Sin tana kara yin mu'amala da hadin gwiwa da kasashen Afirka a fannin albarkatun kwadago sannu a hankali. Mutanen Sin suna kara zuwa Afirka bisa tsarin dandalin hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka. Tun daga shekarar 2004, kasar Sin ta aika da masana da malamai fiye da 500 zuwa kasashen Afirka, don taimakonsu wajen horar da kwararru masu ilmin kimiyya da fasaha na noma da ilmin koyar da sana'o'i da kiwon lafiya, sun ba da gudummawarsu a fannin raya kasashen Afirka, sun kuma kulla hulda da jama'ar Afirka, suna kara hada kansu yadda ya kamata. Shugaban kasar Sudan Omar Hassan El-Bashir ya nuna babban yabo kan wannan, ya ce,'Matasa masu yawa sun shiga cikin zaman al'ummar kasar Sudan, sun kulla kyakkyawar dangantaka tare da jama'ar Sudan, musamman ma matasa. Mun yaba wa irin wannan hadin gwiwa da ke tsakanin jama'a, muna ganin cewa, huldar da ke tsakanin kasashen 2 ba za ta sami ci gaba ba, sai kasashen 2 sun karfafa yin hadin kai a tsakanin jama'a, kamar yadda suka bunkasa dangatakar siyasa da ta tattalin arziki da ciniki. Muna goyon bayan kara hada kammu a wannan fanni.'

Ban da wannan kuma, bangarorin Sin da Afirka sun habaka fannonin hadin gwiwa a shekarun baya da suka shige. Ministan aiwatar da dokoki na kasar Algeria Taib Baleez ya bayani kan wannan cewa,'Dandalin hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka wata dama ce mai daraja ga dukan kasashen Afirka da Sin, ya sa kaimi kan hadin gwiwa a tsakanin bangarorin 2 a fannonin daban daban, wadanda suka hada da aiwatar da dokoki da harkokin shari'a. Kasashen Algeria da Sin sun sa hannu kan yarjejeniyoyi 2 a fannin aiwatar da dokoki, za su kuma cimma yarjejeniyoyi 2 da abin ya shafa ba da dadewa ba.'

Jami'in ma'aikatar harkokin waje ta kasar Masar Tahir Farahat ya bayyana ra'ayinsa kan makomar da Sin da Afirka ke fuskanta wajen yin mu'amalar al'adu, a cewar ya yi, ya kamata kasashen Sin da Afirka su himmantu kan hada kai da yin mu'amala ta fuskar al'adu, su kyautata irin wannan mu'amala ta hanyoyin shirya bukukuwan nune-nune da na sinima dai makamantansu.(Tasallah)