Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-06 18:33:46    
Taron koli na Beijing ya bude sabon hali ga alaka tsakanin Sin da Afirka

cri
A ran 6 ga wata, jaridar People's Daily, wato jarida ce mafi muhimanci a kasar Sin ta bayar da wani sharhi, inda aka nuna cewa, taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin guiwa tsakanin Sin da Afirka ya bude sabon hali ga alakar dangantakar hadin guiwa a tsakaninsu.

Wannan sharhi mai lakabi "Bude sabon hali ga alakar dangantakar hadin guiwa tsakanin Sin da Afirka tare" ya ce, yau da shekaru 50 da suka wuce, sabuwar kasar Sin ta fara raya dangantakar diplomasiyya da kasashen Afirka. A cikin dogon lokacin da ya wuce, ko a cikin gwagwarmayar neman 'yancin al'ummomi da 'yancin kai, ko a cikin gwagwarmayar kiyaye ikon mulkin kasa da yunkurin raya kasa, kasashen Sin da Afirka su kan nuna wa juna tausayi da goyon baya. Yanzu, lokacin da kasar Sin da kasashen Afirka suke fuskantar nauyin raya tattalin arzikinsu da neman bunkasuwarsu, bangarorin Sin da Afirka sun yi tattaunawa sun sami ra'ayi daya na kiran wannan taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin guiwar Sin da Afirka. Sakamakon haka, wannan taro yana da ma'ana mai tarihi sosai wajen hade tarihi da nan gaba.

Sannan kuma, wannan sharhi ya nuna cewa, taron koli na Beijing yana karfafa alakar gargajiya da ke kasancewa a tsakanin jama'ar Sin da kasashen Afirka, kuma yana samar da sabon karfin raya hadin guiwa tsakaninsu, har ma yana sa kaimi wajen cigaban tsarin dandalin tattaunawa kan hadin guiwar Sin da Afirka. Wannan taron koli kuma ya samar da sabon tunani kan yadda za a iya kara yin hadin guiwa a tsakanin kasashe masu tasowa, kuma yana kulla niyyar sada zumunta a tsakanin Sin da Afirka har abada. Yana kuma bayyana sabuwar makomar yin hadin guiwa tsakaninsu. Sabo da haka, wannan taro ya zama sabon abu da ke bayyana hadin guiwar sada zumunta tsakanin Sin da Afirka. (Sanusi Chen)