Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-06 18:32:18    
An fara bikin nune-nunen kayayyakin Afirka a Beijing

cri

A ran 6 ga wata, an fara bikin nune-nunen kayayyakin da masana'antu 170 na kasashen Afirka 23 suka kera a nan birnin Beijing.

Ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ce ta shirya wannan bikin da yake daya daga cikin aikace-aikacen da ke goyon bayan taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin guiwar kasar Sin da kasashen Afirka. Ana ganin cewa, wannan yana alamantar da cewa, kasar Sin tana kara bude kasuwanninta ga kayayyakin kasashen Afirka, kuma tana kara yin musanye-musanyen cinikayya tsakanin Sin da kasashen Afirka.

A gun bikin kaddamar da nune-nunen kayayyakin Afirka, Mr. Jiang Zengwei, mataimakin ministan kasuwanci na kasar Sin ya ce, dalilin da ya sa aka shirya wannan bikin nune-nunen kayayyakin Afirka shi ne, ana son sa kaimi kan masana'antun kasar Sin da na kasashen Afirka da su kara yin musaya da hadin guiwa tsakaninsu. A waje daya kuma, kasar Sin tana son taimakawa masana'antun kasashen Afirka wajen fahimta da budewar kasuwannin kasar Sin. Sabili da haka, za a iya raya hadin guiwar cinikayya tsakanin Sin da Afirka yadda ya kamata.

Kayayyakin Afirka da ake nune-nune a gun bikin suna hade da lu'u lu'u da kayayyakin saka da ma'adinai da kayayyakin fata da kofi da ka fi zabo da ti da dai sauransu. (Sanusi Chen)