Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-06 17:52:44    
Kungiyar farko ta masu aikin sa kai ta lardin Shandong za ta tafi Afirka

cri
A karshen wannan wata, kungiyar farko ta masu aikin sa kai ta lardin Shandong na kasar Sin za ta tashi zuwa kasar Zimbabwei domin yin aikin sa kai a kasar.

Wannan kungiya tana hade da mutane masu aikin sa kai 15 wadanda suke da shekaru tsakanin 20 da 35 da haihuwa, kuma za su yi aikin sa kai a kasar Zimbabwei har na tsawon shekara daya. Wadannan mutane masu aikin sa kai za su yi aiki a kasar Zimbabwei a fannonin kiwon dabbobi da sarrafa amfanin gona da koyar da harshen Sinanci da kuma yin aikin jiyya ta hanyar likitancin gargajiya na kasar Sin.

Tun daga watan Mayu na shekarar 2002, kungiyar matasa masu aikin sa kai ta kasar Sin ta fara aiwatar da shirin tura matasa masu aikin sa kai zuwa kasashen waje. Ya zuwa yanzu, ta riga ta aika da matasa masu aikin sa kai fiye da dari 1 zuwa kasashe masu tasowa ciki har da kasar Laos da ta Myamar. (Sanusi Chen)