Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-06 16:57:03    
kasar Sin tana hadin kanta tare da kasashen duniya wajen kiyaye muhallin teku na duniya

cri

Shugaban babbar hukumar kiyaye muhalli ta kasar Sin Zhou Shengxian ya bayyana a gun wani taron da aka yi a ran 16 ga wata a birnin Beijing, cewa a 'yan shekarun nan da suka gabata, gwamnatin kasar Sin ta samu babban ci gaba a fannin kiyaye muhallin teku, kuma ta rattaba hannu a kan yarjeniyoyin duniya da yawa dangane da kiyaye muhallin teku. Yanzu tana hada kanta tare da kasashen duniya wajen kiyaye muhallin teku na duniya. To, a cikin shirinmu na yanzu, za mu yi muku bayani kan kokarin da kasar Sin ke yi a wannan fanni.

A ran 16 ga wata, a birnin Beijing, babban birnin kasar Sin, an bude taron bincike tsakanin gwamnatocin kasa da kasa a karo na biyu kan shirin duniya na daukar matakin bayar da kariya a yankunan teku daga harkokin da ake yi a doron kasa, wanda aka shafe kwanaki biyar ana yinsa. Wakilan kare muhalli da suka zo daga kasashe fiye da 100 sun halarci taron.

A gun bikin bude taron, shugaban babbar hukumar kiyaye muhalli ta kasar Sin Zhou Shengxian ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin tana mai da hankali sosai kan ayyukan bayar da kariya a yankunan teku daga harkokin da ake yi a doron kasa. Kuma ya ce,

"Kasar Sin tana tafiyar da shirin kawar da kanzantar ruwa a muhimman koguna, da sa kaimi ga kayyade gurbataccen ruwa zuwa teku, da inganta hanyoyin magance gurbatar muhalloli sakamakon dagwalon masana'antu, da rage gurbatar ruwan teku da jiragen ruwa da tasohin jiragen ruwa da kuma sha'anin kiwon kifi da halittu cikin teku ke haddasawa, da inganta gina yankunan kiyaye muhallin halittun teku da dasa bishiyoyi da ke gabobin teku, da kuma karfafa ayyukan gudanar da kiyaye muhallin teku."

Layin gabobin teku na babban yankin kasar Sin ya kai fiye da kilomita dubu 18, kuma yawan tsibiran da ke kusa da gababin teku na kasar Sin ya zarce 6500. Sabo da haka ana iya ganin cewa, kasar Sin tana da makeken haddin ruwa, da kuma albarkatun teku masu yawa. Tare da bunkasuwar tattalin arzikinta, kasar Sin tana karfafa kiyaye muhallin teku. A 'yan shekarun da suka gabata, kasar Sin ta rika kyautata dokoki da kuma manufofin da suka shafi kiyaye muhallin teku, da kuma kara karfin kiyaye muhallin teku. Ban da wannan kuma ta kara fahimtar ma'anar kiyaye muhallin teku na duniya.

Mr. Zhou Shengxian ya bayyana cewa, ban da gudanar da ayyukan kiyaye muhallin tekunta yadda ya kamata, kasar Sin tana hada gwiwa tare da kasashen duniya wajen kiyaye muhallin teku na duniya, kuma ta rattaba hannu a kan yarjeniyoyi masu yawa dangane da kiyaye muhallin teku, kamar "dokokin teku na MDD na shekara ta 1982" da kuma "yarjejeniyar kiyaye halittu iri daban daban ta shekarar 1992" da dai sauransu.

Madam Veerle Vandeweerd, mai shiga tsakani kan shirin daukar matakai a duk duniya ta hukumar kula da kiyaye muhalli ta MDD ta amince da kokarin da kasar Sin take yi wajen bayar da kariya a yankunan teku daga harkokin da ake yi a doron kasa. Kuma ta ce,

"kasar Sin ta yi matukar kokari wajen warware matsalar kazamtar teku. Kasar Sin wata memba ce ta shirin duniya na daukar matakin bayar da kariya a yankunan teku daga harkokin da ake yi a doron kasa. Abin da ya fi faranta mana rai shi ne, dukkan hukummomin da abin ya shafa na kasar Sin sun shiga shirin, ban da wannan kuma kasar Sin ta sa hannu a cikin shirye-shirye masu yawa wajen kiyaye muhallin teku na shiyya-shiyya."

Ko da yake gwamnatin kasar Sin ta gudandar da ayyuka masu yawa a fannin kiyaye muhallin teku, amma za ta fuskanci kalubale mafi tsanani a nan gaba. Yanzu ana gurbatar da wasu haddin ruwan teku na kasar Sin sosai, musamman ma yawan kazamtar da ake zubawa teku ta yi yawa.

Mr. Zhou ya bayyana cewa, a nan gaba kasar Sin za ta ci gaba da gudanar da ayyukan kiyaye muhallin teku kamar yadda ta kan yi kullum, da kuma kara yin cudanya da hadin gwiwa tare da kasashe daban daban a fannin kiyaye muhallin teku.

"kiyaye muhallin teku da albarkatun teku da kuma ingiza bunkasuwa mai dorewa nauyi ne da bai kamata ba kasashen duniya su yi watsi da shi. Kasar Sin za ta hada kanta da kasashen duniya wajen kiyaye muhallin teku na duk duniya ba tare da kasala ba."

Bisa labarin da muka samu, an ce, ban da taron, an kira dandalin tattaunawa na kasa da kasa kan shirin duniya na daukar matakin bayar da kariya a yankunan teku daga harkokin da ake yi a doron kasa. Wakilan kasar Sin da sauran kasashen waje sun yi tattaunawa tare kan kiyaye muhallin teku, da kuma yin koyi da juna kan sakamako mai kyau da suka samu wajen kiyaye muhallin teku da kuma hadin gwiwa tsakanin shiyya-shiyya.(Kande Gao)