|
 |
 |
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
 |
|
 |
|
|
 |
(GMT+08:00)
2006-11-06 16:45:39
|
An bude taron baje koli na kayayyakin Afrika a nan birnin Beijing
cri
Ran 6 zuwa ran 7 ga wata a nan birnin Beijing, an shirya "taron baje koli na kayayyakin Afrika" da ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta dauki nauyin. Masana'antu 170 da suka fito daga kasashe 23 na Afrika sun halarci taron.
Taron ya mai da hankali sosai kan nuna kayayyaki masu kyau na kasashen Afrika, kamar su: lu'u lu'u, da kayayyakin saka, da ma'adinai, da dai sauransu. A cikin lokacin taron, kasashen Nijeriya, da Tunis, da Uganda, da kuma sauran kasashe za su shirya taron musamman, domin gabatar da halin da kasashen Afrika da abin ya shafa ke ciki wajen ciniki da zuba jari, da muhallin kasuwanni, da kuma albarkatun ma'adinai, da kofi, da kuma sauran kayayyakun musamman. (Bilkisu)
|
|
|