Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-06 16:40:24    
kabilar De'ang

cri

An fi samun 'yan kabilar De'ang a cikin yankin Dehong na kabilun Dai da Jingpo mai cin gashin kai da ke jihar Yun Nan ta kasar Sin da dai sauran wurare da yawa na jihar. Murabba'in wuraren da 'yan kabilar De'ang ke da zama ya kai kilomita fiye da dubu 30, sabo da haka ana ganin cewa, kabilar De'ang wata kabila ce da mutanenta su kan yi zamansu a wurare daban daban, ba safai su kan yi zama tare ba. Yawacin 'yan kabilar suna da zama tare da kabilun Jingpo da Wa da Han da sauran kananan kabilun Sin. Bisa kidayar yawan mutanen kasar Sin a karo na biyar da aka yi a cikin shekara ta 2000, yawan 'yan kabilar De'ang ya kai dubu 17. 'Yan kabilar Dai suna yin amfani da harshensu, amma ba su da harafin kabilar.

A farkon kafuwar kasar Sin, gwamnatin kasar ta aika da kungiyar aiki ta kananan kabilu zuwa yankin kabilar De'ang domin sanar da manufofin Jam'iyyar Kwaminis ta Sin kan kananan kabilu da kuma ba da taimako gare su wajen raya sha'anin noma. A cikin shekara ta 1956, bisa halin daban daban da wuraren kabilar De'ang ke ciki kan bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'umma, gwamnatin ta dauki matakai daban daban dom yin gyare-gyaren demokuradiyya a yankin kabilar. Kuma bayan gyare-gyaren, 'yan kabilar De'ang sun fara bin hanyar gurguzu, kuma an samun bunkasuwa cikin sauri kan harkokin siyasa da tattalin arziki da al'adu. Ban da wannan kuma a cikin gwamnatocin wuraren da aka fi samun 'yan kabilar De'ang, akwai ma'aikatan gwamnati na kabilar, bugu da kari kuma a gun babban taron wakilan jama'ar kasar Sin, akwai wakilan 'yan kabilar De'ang.

A cikin yankin kabilar, dukkan yaran da ya kamata su shiga makaranta suna da zafarin karatu. An kafa asibitoci a cikin yankin, kuma an horar da malamai da likitoci da kwararrun kimiyya da fahasa na kabilar da yawa.

Jama'a masu sauraro, yanzu sai ku huta kadan, bayan haka kuma za mu karanta muku wani bayani kan cewa, 'Yan kabilar Tibet da ke yin amfani da harshen Amdo sun cimma burinsu wajen kallon talibijin.(Kande)