Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-06 16:37:40    
Shugabannin kasashen Afrika sun jinjina sosai ga taron koli na Beijing

cri
A cikin 'yan kwanakin da suka wuce, shugabanni da kafofin watsa labaru na kasashen Afrika sun ci gaba da yin jinjina sosai ga taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan harkokin hadin kai a tsakanin Sin da Afrika, suna ganin cewa, shugabannin kasar Sin da na kasashen Afrika sun taru a nan birnin Beijing, kuma sun tattauna manyan manufofin bunkasuwa, wannan yana da ma'ana sosai.

Ran 5 ga wata, Mr. Jakaya Mrisho Kikwete, shugaban kasar Tanzania, wanda ya halarci taron kolin ya ce, kasashen Afrika suna bukatar kasuwa cikin gaggawa domin sayar da kayayyakinsu, yanzu suna kokarin jawo jari da fasaha, kuma suna fatan rage basussuka da suka ci. Matakai 8 da gwamnatin kasar Sin za ta dauka, wadanda Mr. Hu Jintao, shugaban kasar Sin ya gabatar a wannan dandalin tattaunawa, dukansu suna nasaba da matsalolin da suka fi jawo hankulan kasashen Afrika. Afrika za ta samu moriya daga matakan nan.

Ran 5 ga wata, jaridar The Standard ta kasar Kenya ta bayar da labari, inda ta bayyana alkawari da gwamnatin kasar Sin ta dauka game da ba da gudummowa iri iri ga Afrika a taron kolin, kuma ta jaddada cewa, kasar Sin ta gabatar da wadannan taimako ba tare da sharuda ba, wannan yana da bambanci da kasashen yamma, wannan kuma dalilin da ya sa shugabannin kasashen Afrika suka mai da hankali sosai kan wannan taron koli.

Bayan haka kuma, a ran 4 ga wata, jaridar Times Of Zambia ta kasar Zambia, da kamfanin dillancin labaru na Gabas ta tsakiya na kasar Masar, da kuma sauran kafofin watsa labaru na Afrika sun yi sharhi daya bayan daya, inda suke ganin cewa, taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan harkokin hadin kai a tsakanin Sin da Afrika zai karfafa hadin kan Sin da Afrika wajen tattalin arziki da ciniki, kuma zai ingiza bunkasuwar sabbin manyan tsare-tsaren dangantakar abokataka da ke tsakanin Sin da Afrika. (Bilkisu)