Ran 5 ga wata, a nan Beijing, ministan harkokin waje na kasar Sin Li Zhaoxing ya bayyana cewa, hadin gwiwar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka ya dace da manyan bukatun 'Kundin Tsarin Majalisar Dinkin Duniya' sosai.
A gun taron manema labaru da ya yi tare da takwarorinsa na kasashen Habasa da Masar a ran nan, Mr. Li ya bayyana cewa, kasar Sin tana himmantuwa kan raya dangantakar abokantaka da ke tsakaninta da kasashen Afirka, wato tana himmantuwa kan ingiza hadin gwiwa don moriyar juna a tsakaninsu don tabbatar da samun ci gaba tare da kyautata zaman rayuwar jama'ar bangarorin 2, bisa muhimman ra'ayoyi na 'Kundin Tsarin Majalisar Dinkin Duniya'. Kasar Sin da kasashen Afirka suna hada kansu ne ba domin wani daban ba, ba su kyamar wani daban ba, sa'an nan kuma, ba su kawo wa moriyar sauran kasashen illa da barazana ba. Cikin sahihanci ne kasar Sin tana fatan kasashen Afirka za su sami ci gaba cikin lumana. A sa'i daya kuma, bisa tushe na bude kofa da yin hadin gwiwa ne kasar Sin tana son yin kokari tare da kasashen duniya wajen ba da gudummawa kan ganin cewa, Afirka tana samun ci gaba cikin lumana.(Tasallah)
|