Ran 5 ga wata, a nan Beijing, ministan harkokin waje na kasar Sin Li Zhaoxing ya bayyana cewa, hadin gwiwar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka yana amfana wa bangarorin 2.
A gun taron manema labaru da ya yi tare da takwarorinsa na kasashen Habasa da Masar a ran nan, Mr. Li ya bayyana cewa, anihin hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da Afirka a fannonin tattalin arziki da ciniki da kuma sha'anin zaman al'ummar kasa shi ne yin zaman daidai wa daida da moriyar juna da kuma taimakon juna. Ya kara da cewa, kasar Sin da kasashen Afirka suna fuskantar damar bunkasuwa mai kyau, a sa'i daya kuma, suna fuskantar kalubale iri daban daban da kuma iri daya. Bangarorin Sin da Afirka za su daidaita su yadda ya kamata a sakamakon yin hadin gwiwa a tsakaninsu.(Tasallah)
|