Ran 5 ga wata, a nan Beijing, mataimakawan ministan kasuwanci na kasar Sin Fu Ziying ya bayyana cewa, an kiyasta cewa, jimlar kudaden da kasar Sin za ta samu daga wajen yin cinikayya da kasashen waje za ta kai misalin dalar Amurka biliyan 1,700 a shekarar da muke ciki.
A gun taron ba da rahoto kan bunkasuwar sana'oin kasar Sin ta shekarar 2007 da aka yi a ran nan, Mr. Fu ya bayyana cewa, tun daga farkon wannan shekara har zuwa yanzu, kasar Sin tana samun saurin bunkasuwar ciniki a tsakaninta da kasashen waje, tana kuma ta kara girman ciniki. Adadin da ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta bayar ya nuna cewa, tun daga watan Janairu zuwa na Satumba na wannan shekara, jimlar kudaden da kasar Sin ta samu daga wajen yin ciniki da kasashen waje ta kai dalar Amurka fiye da biliyan 1270.(Tasallah)
|