Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-04 18:18:08    
An bude taron tattaunawa a tsakanin shugabannin Sin da Afrika, da shugabannin bangarorin masana'antu da kasuwanci

cri

Ran 4 ga wata a nan birnin Beijing, an bude taron tattaunawa a tsakanin shugabannin Sin da Afrika da shugabannin bangarorin masana'antu da kasuwanci, da babban taron kwararrun masana'antun Sin da Afrika na karo na biyu, masu kula da harkokin masana'antu da kasuwanci, da kuma wakilan kwararrun masana'antu na Sin da kasashe daban daban na Afrika fiye da dubu sun halarci bikin bude taron.

Mr. Wen Jiabao, firayin ministan kasar Sin, da wasu shugabannin kasashen Afrika sun halarci bikin bude babban taron. Mr. Wen Jiabao zai bayar da jawabi kan babban jigon taron nan. Mr. Meles Zenawi, firayin ministan kasar Habasha shi ma zai yi jawabi.

Bayan bikin bude taron, kwararrun masana'antun Sin da Afrika za su yi shawarwari kan fannonin da ke dacewa, kuma masana'antun da ke da nufin hadin kansu, za su daddale yarjejeniyoyi. (Bilkisu)