Ran 3 ga wata, a nan birnin Beijing, Malam Gobind Nankani, mataimakin shugaban Bankin Duniya mai kula da harkokin nahiyar Afrika ya bayyana cewa, kasar Sin tana kara ba da babban taimakonta ga kasashen Afrika don bunkasa harkokin tattalin arzikinsu ta hanyar cinikiya da zuba jari.
Yayin da Nankani ke karbar ziyara da manema labaru suka yi masa, ya bayyana cewa, an sami babban ci gaba wajen inganta hadin guiwar tattalin arziki da ciniki a tsakanin Sin da kasashen Afrika cikin shekarun nan da suka wuce, yawan kudin jari da kasar Sin ta zuba a nahiyar Afrika ya dauki kashi 10 cikin dari bisa jimlar kudin jarin nan. Yanzu, kasashen Afrika suna cin gajiyar kudin jari da kasar Sin ke kara zubawa. Ya gabatar da shawara ga kasashen Afrika da su dauki matakai masu yakini don kara rage yawan kudi da suke kashewa wajen yin cinikayya, da kyautata manyan ayyukansu da guraben zuba jari, ta yadda za su kara jawo kudin jari daga kasar Sin. (Halilu)
|