Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-04 12:20:57    
An fara taron koli na Beijing tsakanin Sin da kasashen Afirka

cri

A ran 4 ga wata da safe, an fara taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin guiwar kasar Sin da kasashen Afirka. Shugaban kasar Sin Hu Jintao da shugabannin kasashe ko gwamnatoci na kasashen Afirka 48 da wakilan kungiyoyin kasa da kasa, ciki har da Mr. Meles Zenawi, firayin ministan kasar Habasha wadda ke shugabantar wannan taron dandalin tattaunawa kan hadin guiwar kasar Sin da kasashen Afirka tare da kasar Sin sun halarci taron. Mr. Meles Zenawi, da kuma Denis Sassou-Nguesso, shugaban kasar Congo Kinshasha, kuma shugaba na yanzu na kungiyar tarayyar Afirka sun kuma bayar da jawabai bi da bi.

A gun bikin kaddamar da taron, shugaba Hu Jintao ya jaddada cewa, sada zumunta da aminci tushe ne mai karfi ga dinga karfafuwar alaka a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka ba tare da kasala ba. Zaman daidai wa daida, muhimmin tushe ne da ke tabbatar da kara amincewar juna tsakaninsu. Bugu da kari kuma, nuna wa juna goyon baya, dalilin da ya sa ne dangantakar hadin guiwa da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka ta kara ta samun cigaba. A waje daya kuma, neman bunkasuwa tare, buri daya ne da jama'ar kasar Sin da kasashen Afirka suke nema cimmawa a kai.

Mr. Hu ya kuma bayyana cewa, kasar Sin da kasashen Afirka za su kara yin hadin guiwa a fannoni daban-daban domn kara raya sabuwar alakar dangantakar abokantaka a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka.

Bugu da kari kuma, Mr. Hu ya bayar da manufofi 8 da gwamnatin kasar Sin za ta dauka domin ciyar da sabuwar alakar dangantakar abokantaka a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka.

A cikin nasa jawabi, Mr. Zenawi ya ce, an yi wanna taron koli ne lokacin da ake taya murnar cikon shekaru 50 da kafuwar dangantakar diplamasiyya a tsakanin sabuwar kasar Sin da kasashen Afirka. Wannan taron koli ya bayyana wa duk duniya niyyar raya sabuwar alakar dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a tsakanin Sin da kasashen Afirka.

Mr. Sassou ya kuma bayyana cewa, ko da yake dandalin tattaunawa kan hadin guiwar kasar Sin da kasashen Afirka ya yi shekaru 6 kawai. Amma yana da muhimmin amfani a fannonin siyasa da tattalin arziki da zamna al'umma da al'adu ga bangarorin biyu. (Sanusi Chen)