Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-03 18:34:17    
An bude taron ministoci na dandalin tattaunawa kan hadin guiwar Sin da Afrika

cri

Ran 3 ga wata a nan birnin Beijing, an bude taron ministoci na karo na uku na dandalin tattaunawa kan hadin guiwa a tsakanin Sin da Afrika. Ministocin harkokin waje da ministoci masu kula da harkokin hadin guiwar tattalin arziki da wakilai na Sin da kasashen Afrika 48 sun halarci taron. Madam Wu Yi, mataimakiyar firayim ministar kasar Sin ta yi jawabi a gun bikin bude taron cewa, ya kamata, Sin da Afrika su yi ta kyautata tsarin dandalin tattaunawa kan hadin guiwarsu bisa ka'idojin yin tattaunawa cikin daidaici, da moriyar juna, da sassaucin ra'ayi da kuma sannu a hankali, su inganta hadin guiwarsu a karkashin inuwar tsarin nan.

Bayan haka ta kara da cewa, "ya kamata, Sin da Afrika su yi ta takaita kyakkyawan sakamako da matakai da suka dauka wajen kafa tsarin dandalin tattaunawa kan hadin guiwarsu da yin hadin kansu ta fuskar aminci a cikin shekarun nan 6 da suka wuce. Su tsara fasalin nan gaba a tsanake, su nuna himma ga aiwatar da matakai da za a dauka, ta yadda dandalin tattaunawar zai zama wata tuta ga hadin guiwar Sin da Afrika a fannoni daban daban."

Daga nan ne, Madam Wu Yi ta nuna cewa, taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin guiwar Sin da Afrika da za a yi nan gaba kadan wani muhimmin al'amari ne ga tarihin dangantakar da ke tsakanin Sin da Afrika, kuma zai ciyar da aminci a tsakanin Sin da Afrika gaba daga duk fannoni.

Malam Li Zhaoxing, ministan harkokin waje na kasar Sin da Malam Bo Xilai, ministan kasuwanci na kasar da Malam Seyoun Mesfin, ministan harkokin waje na kasar Habasha wadda take daya daga cikin kasashe masu shugabantar dandalin tattaunawar, da kuma Malam Sofian Ahmed, minista mai kula da aikin kudi da harkokin raya tattalin arziki na kasar Habasha ne suka shugabanci taron ministocin. A cikin jawabinsa, Malam Li Zhaoxing ya bayyana cewa, "gobe, za a bude taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin guiwar Sin da Afrika wanda muka dade muke jiransa. Taron zai zama wani gagarumin taro mai matukar muhimmanci da shugabannin Sin da na kasashen Afrika za su yi. Bari mu yi kokari tare, kuma a tsanake, mu kammala duk ajandar wannan taron ministoci da kyau, don aza kyakkyawan harsashi ga yin taron koli na Beijing tare da nasara."

A madadin kasashen Afrika, Malam Seyoun Mesfin ya bayar da jawabinsa cewa, tun bayan da aka fara yin taron dandalin tattaunawa a kan hadin guiwar Sin da Afrika a cikin shekaru 6 da suka wuce, an inganta ma'amala da hadin guiwa a tsakanin Afrika da Sin, bangarorin biyu sun hada kansu da kyau a manyan fannoni daban daban kamar cinikayya da zuba jari da horar da kwararru da sauransu, sun nuna wa juna fahimta a kan harkokin duniya, kuma sun yi ta kara samun daidaituwa a tsakaninsu. Ya kara da cewa, "kiran taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin guiwar Sin da Afrika wani babban al'amari ne mai muhimmanci a cikin tarihi. An daga taron ministocin nan zuwa taron koli, wannan ya nuna burin Afrika da Sin na kokarin inganta hadin guiwarsu. Halartar taron koli da shugabannin kasashen Afrika da yawa za su yi, ya shaida cewa, kasashen Afrika suna dora muhimmanci sosai ga dandalin tattaunawar nan. Bangarorin nan biyu dukanninsu sun amince da cewa, kara inganta dandalin tattaunawar nan yana amfanawa bangarorin Sin da Afrika gaba daya."

Wannan taron ministoci ya dudduba "shirin sanarwar taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin guiwar Sin da Afrika" da "shirin daukar matakai na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin guiwar Sin da Afrika a tsakanin shekarar 2007 zuwa ta 2009", da sauran takardu, kuma ya zartas da su. Taron ya kuma yanke shawara cewa, za a shirya taron ministoci na karo na hudu na dandalin tattaunawa kan hadin guiwar Sin da Afrika a kasar Masar a shekarar 2009. (Halilu)