Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-03 16:35:08    
Ayyukan share fage ga gudanar da taron wasannin Olympic na Beijing sun samu yabo daga kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa

cri

An yi zama na 7 na kwamitin daidaituwa na taron wasannin Olympic na 29 na yanayin zafi na kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa a kwanakin baya ba da jimawa ba a nan birnin Beijing, inda kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing ya gabatar da wani rahoto ga kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa kan yadda ake share fage ga gudanar da taron wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008. Ban da wannan kuma, bangarorin biyu sun yi shawarwari tsakaninsu kan takamaiman ayyuka na nan gaba. Bayan da aka yi ziyarar gani da ido da kuma yin shawarwari, sai kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa ya buga taken cewa, ana aiwatar da aikin share fage ga yin taron wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008 daidai bisa tsarin da aka tsara, wato ke nan bangaren Beijing yana cika alkawarin da ya yi a da lokacin da yake neman shirya taron wasannin Olympic.

Jama'a masu saurare, kuna sane da, cewa kwamitin daidaituwa na taron wasannin Olympic na 29 na yanayin zafi, wata hukuma ce ta musamman ta kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa, wadda kuma ke bada jagoranci da taimako da kuma sa ido kan ayyukan share fage ga gudanar da taron wasannin Olympic na Beijing na shekarar 2008. Kafin a gudanar da wannan gagarumin taro, wannan kwamiti yakan yi zaman taro sau biyu a kowace shekara a nan Beijing. A gun taron da aka yi a wannan gami, kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing ya gabatar da wani rahoto ga kwamitin shirya taron wasannin Olympic na kasa da kasa kan ayyukan da aka yi a rabin farkon wannan shekara na share fage ga gudanar da taron wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008. A gun taron ganawa da manema labarai da aka shirya kafin a rufe taron, kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa ya ce, ya lura da, cewa bisa kokarin da kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing yake yi, an samu ci gaba a wassu jerin fannoni wajen gudanar da ayyukan share fage ga yin taron wasannin Olympic na Beijing, wato an samu sakamako mai tsoka wajen gina dakuna da filayen wasannin Olympic lami-lafiya; sa'annan an samu nasara wajen shirya gasar tseren kwale-kwale ta Qingdao da kuma gasar cin kofin duniya ta 11 ta wasan softball na mata. Saboda haka, an tattara wassu kyawawan fasahohi wajen shirya gasanni. Ban da wadannan kuma, yanzu ana yin ayyukan shirye-shirye na bikin bai wa juna wutar yula na taron wasannin Olympic na Beijing da kuma bukukuwan bude shi da na rufe shi kamar yadda ya kamata; Kazalika, an soma yin ayyukan share fage ga gudanar da taron wasannin Olympic na nakasassu na Beijing daga dukkan fannoni; Sa'annan ayyukan daukar mutane masu sa kai na taron wasannin Olympic da kuma taron wasannin Olympic na nakasassu sun samu amsa cikin fara'a daga duk al'ummar kasar; Dadin dadawa, an kara kyautata aikin kiyaye muhalli.

' Yan kwamitin daidaituwa na taron wasannin Olympic na 29 na yanayin zafi na kwamitin taron wasannin Olympic na kasa da kasa sun kai ziyarar gani da ido zuwa dakin wasanni mai siffar "gidan tsuntsu" da ake kira " bird's nest" da kuma dakin wasanni mai siffar "tafkin wanka" da ake kira "cubic water" a Turance da kuma dakunan wasannin motsa jiki na wassu jami'o'i da kolejoji; Ban da wannan kuma sun saurari rahotannin da kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing ya gabatar kan sauran ayyukan share fage..

Mr. Hein Verbruggen, shugaban kwamitin daidaituwa na taron wasannin Olympic na 29 na yanayin zafi ya nuna gamsuwa sosai ga ayyukan share fage da kwamitin shirya taron wasannin Olympic yake yi. Sa'annan ya fadi, cewa lallai gwamnatin kasar Sin da kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing sun cika alkawarinsu na gudanar da wani taron wasannin Olympic dake da sigar musamman kuma bisa matsayin koli. Mr. Verbruggen ya ce, kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa ya yi farin ciki da ganin cewa, a ran 1 ga watan Oktoba na wanna shekara, shugaban kasar Sin Mr. Hu Jintao ya yi ziyarar duba aikin gina dakuna da kuma filayen wasanni na Olympic, inda ya yi muhimmin jawabi. Wannan dai ya kasance tamkar goyon baya da kuma himmantawa ne ga gwamnatin Beijing wajen gudanar da taron wasannin Olympic cikin nasara.

Firaminista Wen Jiabao na kasar Sin shi ma ya gana da shugaban kwamtin wasannin Olympic na kasa da kasa wato Mr. Jacques Rogge, inda ya jaddada, cewa gwamnatin kasar Sin za ta sauke nauyin dake bisa wuyanta na yin hidima da kyau bisa dokokin kasashen duniya ga 'yan wasa, da jami'ai, da kafofin watsa labaru da kuma 'yan kallo daga kasashe da jihohi daban daban na duniya.

Bisa shirin da aka tsara, an ce, a shekara mai zuwa, ayyukan share fage ga gudanar da taron wasannin Olympic na Beijing za su shiga matakin gwaji da na jarrabawa daga dukkan fannoni. (Sani Wang )