Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-03 12:46:29    
Jakadun kasashen Afrika na sa ran alherin cewa ' taron koli na Beijing' zai bude sabon matakin hadin gwiwar dake tsakanin  Sin da Afrika

cri

Za a gudanar da gagarumin taron koli na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika gobe Asabar a nan birnin Beijing. A gabannin ranar bude taron, jakadun kasashen Afrika dake kasar Sin sun sha bayyana, cewa taron kolin na Beijing zai zama tamkar sabuwar alama ta kyakkyawar dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika. Suna yin kyakkyawan bege ga wannan taro.

Jama'a masu saurare, kuna sane da, cewa kasar Masar, kasa ce ta farko a Afrika wadda ta kulla dangantakar diplomasiyya tare da sabuwar kasar Sin. Lallai ba a manta ba, a shekarar 1956, gwamnatin kasar Masar ta yi watsi da katanga iri daban daban da kasashen yamma suka kafa, ta kulla huldar diplamasiyya tare da Jamhuriyar Jama'ar Sin ba tare da yin wata-wata ba. Wannan dai ya zama wani kyakkyawan labari a cikin tarihin harkokin waje na kasa da kasa. Jakadan kasar Masar dake kasar Sin wato Mahmoud Allam ya furta, cewa ' Taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika da kuma sauran jerin tarurruka na dandalin tattaunawa, za a gudanar da su ne daidai a albarkacin ranar cika shekaru 50 da aka kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika. Mu 'yan kasar Masar mun yi alfahari a kai domin kasarmu ta zama kasa ta farko ta Afrika da ta amince da kasar Sin. Babu tantama, halartar taron kolin da kuma ziyarar aiki da shugaba Mubarak zai yi a kasar Sin, ita ma za ta ciyar da dangantakar dake tsakanin kasar Sin da Masar gaba'.

Sa'annan jakada Mahmoud Allam ya sa ran alheri ga taron koli na Beijing. Ya fadi, cewa kasar Masar ta tattara kyawawan fasahohi a cikin yunkurin raya nahiyar Afrika. Labuddah za ta taka muhimmiyar rawa wajen mayar da kasar Sin da kasashen Afrika don su zama manyan abokai ; Kazalika, kasar Masar tana fatan za a shigo da hajoji masu yawan gaske cikin kasuwannin kasar Sin daga Masar ta hanyar nune-nunen da ake yi yanzu a nan Beijing lokacin da ake gudanar da taron kolin.

Mr. Mirghani Mohamed Salih, jakadan kasar Sudan dake kasar Sin ya fada wa wakilinmu, cewa kyakkyawar dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika tana da dauwamammen tarihi ; Gwamnatin kasar Sin tana goyon bayan gwagwarmayar neman samun mulkin kan al'umma da jama'ar Afrika suke yi ; Daga nasu bangaren, kasashen Afrika su ma suna nuna tsayayyen goyon baya ga kasar Sin a Majalisar Dinkin Duniya. A cikin sabon lokaci na tarihi, kasar Sin da kasashen Afrika dukansu suna dukufa kan bunkasa tattalin arziki. Ko shakka babu dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika zai taka muhimmiyar rawa wajen kara kyautata irin wannnan kyakkyawar hulda. Jadaka Salih ya kara da cewa : ' Babbar nahiyar Afrika, wata ni'imtacciyar nahiya ce, inda akwai albarkatai na kayayyaki da na 'yan kwadago masu yawan gaske. Taron kolin zai kai kyakkyawar dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika zuwa wani sabon mataki'.

Mr. Djamel Eddine Grine, jakadan kasar Aljeria dake kasar Sin shi ma ya fadi albarkacin bakinsa kan dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa dake tsakanin kasar Sin da Afrika, inda ya furta, cewa : ' Wannan dandalin tattaunawa ya riga ya zama kamar wani tsari ne mai amfani na hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika, wanda kuma ya gajarta nisan tsakaninsu. Kasar Sin amintacciyar abokiya ce ta kasashen Afrika. Shugababannin kasashe daban daban za su hadu gu daya a nan Beijing a karo na farko domin tattauna muhimman al'amura.'

( Sani Wang )