
Ran 3 ga wata, a nan Beijing, an bude taron ministoci karo na 3 na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, wakilan kasar Sin da na dukan kasashe 48 na Afirka mambobin dandalin sun halarci wannan taro.

Ministan harkokin waje na kasar Sin Li Zhaoxing da takwaransa na kasar Habasha Seyoum Mesfin da ministan kudi da bunkasuwar tattalin arziki na kasar Habasha Sofian Ahmed da ministan kasuwanci na kasar Sin Bo Xilai sun shugabanci wannan taro daya bayan daya. Mataimakiyar firayin ministar kasar Sin madam Wu Yi ta halaci taron ministoci ta kuma yi jawabi.(Tasallah)
|