Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-02 22:29:24    
Mutanen gida da na waje sun tabbatar da matakan da gwamnatin kasar Sin ta dauka don kiyaye al'adun Tibet

cri

Daga ranar 10 zuwa ranar 19 ga watan Oktoba, an shirya taron dandalin tattaunawa kan al'adun Tibet, kwararru da shahararrun mutane wajen yin nazari kan al'adun Tibet da yawansu ya kai 120 kuma suka zo daga kasashe 12 sun yi tattaunawa kan yadda za a kiyaye da raya al'adun Tibet. Yawancin mahalartan taron sun bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin ta sami sakamako sosai wajen kiyaye al'adun gargajiya na jihar Tibet, ya kamata a tabbatar da sakamakon nan.

Wani mutumi mai suna Jampal Gyatso kuma dan asalin kabilar Tibet da ke da shekaru 68 da haihuwa shi ma ya halarci taron. Tun daga shekaru 80 na karnin da ya shige har zuwa yanzu, yana aikin nazarin al'adun gargajiya na Tibet. Ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin ta ware kudade da yawa tare da aika da ma'aikata da yawa don kiyaye al'adun gargajiya na Tibet, musamman ma an sami sakamako da duk duniya ke zura ido a kai wajen daidaita wakokin tarihi da ke da tsawon jimloli da kalmomi fiye da sauran wakoki a duniya wadanda suke da lakabi haka: Gesar. Yanzu, ma'aikatar al'adu ta kasar Sin ta riga ta jera wakar Gesar cikin sunayen abubuwan al'adu na tarihi ba na kayayyaki ba na rukunin farko .

Mr Jampal Gyatso ya kuma bayyana cewa, kasar Sin ta ware kudade da yawa da kuma aika ma'aikata da yawa don kiyaye al'adun gargajiyarmu, musamman ma wajen kiyaye abubuwan al'adun garagajiya na tarihi ba na kayayyaki ba, wannan ya jawo hankulan bangarori daban daban na zamantakewar al'umma, musamman ma wakar tarihi na "Gesar" tana da ingancin tushen jama'a da tarihi mai dogon lokaci, an sami sakamako mai kyau wajen tattara ta da daidaita ta, shi ya sa mutanen rukunoni daban daban sun nuna yabo sosai a kan aikin.ya kamata mu ci gaba da kokari don kara tattara takardun da aka ajiye su dangane da wakar .

Ba sau daya ba ba sau biyu ba wani shehun malamin jami'ar Griffith ta kasar Australiya mai suna Colin Mackerras ya sauka jihar Tibet , abubuwan da ya ji ya gani sun bayyana cewa, bisa goyon bayan gwamnatin kasar Sin ne, al'adun gargajiyar Tibet ya sami bunkasuwa. Ya ce, a shekarar 1990 da 1997 da 2002, wato sau uku ke nan na kai ziyara a yankunan kabilar Tibet da ke jihar Tibet da lardunan Qinghai da Yunnan da Schuan da saruan wurare na kasar Sin, ni kaina na sa ido ga yadda al'adun gargajiyar Tibet ya sami bunkasuwa sosai, yanke shawarar da rukunonin kasashen yamma suka yi ne ba bisa adalci ba kuma tare da rashin daukar nauyi bisa wuyansu . a yanayin zafi na shekarar 1995, na yi farin ciki da samun damar shiga shagalin murnar bikin gargajiya da aka shirya a wani kauyen da ke nesa da birane a lardin Qinghai, ba ma kawai na ga raye-rayen gargajiyar da aka yi a wurin ba, hatta ma na kallaci bukukuwan addinai irin na gargajiya. Hakikanan abubuwa sun shaida cewa, ba ma kawai al'adun Tibet bai bace ba, har ma al'adun Tibet na gargajiya sun sami bunkasuwa sosai bisa yunkurin goyon baya da gwamnatin kasar Sin take sanyawa.

A gun taron dandalin, wani mamban majalisar hadadiyyar kungiyar kiyaye da raya al'adun gargajiya na Tibet mai suna Lai Shanglong ya bayyana cewa, hakikanan abubuwa da yawa sun bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin ta riga ta maido da bunkasuwar zamantakewar al'umma a gaban kome, gwamnatin ta ware kudade da yawa don gyarawa da kuma gina manyan ayyuka da yawa da sauran gine-ginen ba da ilmi da na kiwon lafiya da suke da nasaba da zamantakewar al'umma. A sa'I daya kuma, al'adun wuraren kasar sun sami girmamawa da karewar da aka yi musu sosai. A takaice dai, gwamnatin kasar Sin ta mai da hankali sosai ga abubuwan da aka samu bisa sanadiyar al'adu wajen raya kasar, an yi kokarin rage cikas da aka kawo musu, da kuma yin kokarin kiyaye kalmomi da zane-zane da wake-wake da wasannin kwaikwayo da likitanci da magungunan sha da addinai da sauran abubuwa na gargajiyar Tibet.(Halima)