Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-02 20:51:06    
Ra'ayi da tsohon jakadan kasar Massar a kasar Sin ya gabatar a kan hadin guiwar kasar Sin da Afrika

cri

A kwanakin baya, wakilan gidan rediyo kasar Sin sun kai ziyara ga Malam Ali Husaam al-Hifni, mataimakin ministan harkokin waje na kasar Masar kuma tsohon jakadan kasar a kasar Sin don jin ta bakinsa dangane da hadin guiwar kasar Sin da Afrika. Da farko, Malam Hifni ya waiwayi hanyar da aka bi wajen aiwatar da dangantaka da ke tsakanin Sin da Afrika a cikin shekaru 50 da suka wuce. Bayan haka ya jiku sosai da cewa, "tun fil azal, ya kasance da hulda a tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika. A shekarar nan muna taya murnar ranar cika shekaru 50 da aka kulla irin wannan hulda. Kasarmu tana matukar jin farin ciki da ganin cewa, a shekarar 1956, kasar Masar ta zama ta farko ta kulla huldar diplomasiya a tsakaninta da Jamhuriyar Jama'ar Sin a cikin duk kasashen Afrika da na Larabawa. "

Malam Hifni yana ganin cewa, yanzu, an riga an fara yin hadin guiwa a tsakanin Sin da kasashen Afrika daga duk fannoni, don yalwata huldar siyasa a tsakaninsu. Ban da ma'amalar gargajiya da ake yi a fannin tattalin arziki da ciniki, kuma hadin guiwar fasaha da ake yi a tsakanin bangarorin nan biyu ya zama wani kyakkyawan abu ga hadin guiwarsu a kwanakin nan. Ya kara da cewa, "hadin guiwa a tsakanin Sin da kasashen Afrika wani sashe ne mai muhimmanci sosai ga bunkasuwar dangantaka a tsakaninsu, kuma ya sami ci gaba sosai. Abin da ya cancanci ambata shi ne, hadin guiwar fasaha da ake yi a tsakaninsu. Kasar Sin ta taba shirya kososhi da yawa wajen horar da 'yan fasaha domin kasashen Afrika, ta yadda za su kara fahimtci sakamako da kasar Sin ta samu wajen bunkasa harkokin tattalin arziki, da jawo kudin jari daga kasashen waje, da kawar da gurbacewar muhalli, da bunkasa matsakaita da kananan masana'antu, da yin cinikin waje, da kara fitar da kayayyaki masu yawa zuwa kasashen waje, da binciken kimiya a fannoni daban daban da sauransu. Abin da ake nufi "binken kimiyya a fannoni daban daban" shi ne, ba ma kawai hukumomin gwamnati ke yin haka ba, har ma masana'antu masu zaman kansu ma suna yi. Haka kuma ba ma kawai gwamnatin kasa ke yi ba, har ma kananan hukumomi na jihohi da birane suna yi."

Bayan haka, Malam Hifni ya ci gaba da cewa, ban da babban ci gaba da aka samu wajen hadin guiwar fasaha a tsakanin Sin da kasashen Afrika, kuma an sami ci gaba sosai wajen yin hadin guiwarsu a fannin tattalin arziki da ciniki.

Dangane da surutun banza da wasu kafofin watsa labaru na kasashen yammaci suka barbaza, wai "kasar Sin na wasosin albarkatun kasa a Afrika", kuma tana gudanar da sabon mulkin Mallaka", Malam Hifni ya tsaya tsayin daka wajen kayatar da wannan surutun banza. Ya bayyana a fili cewa, hadin guiwa a tsakanin Sin da kasashen Afrika mataiki ne da aka dauka bisa tushen taimakon juna don samun moriyar juna, kuma ba tare da wani sharadin siyasa ba.

Malam Hifni ya karasa da maganarsa cewa, "ana aiwatar da hulda a tsakanin Sin da Afrika ne ta hanyoyi daban daban kuma a fannoni daban daban. A zahiri, an sami ci gaba wajen aiwatar da huldar nan, Ko shakka babu, taron dandalin tattaunawa a kan hadin guiwar Sin da Afrika da za a shirya zai gaggauta yalwata irin wannan huldar hadin kai daga duk fannoni. Kasar Masar da sauran kasashen Afrika suna matukar yin farin ciki da ganin haka, kuma suna fatan za a ci gaba da yalwata irin wannan huldar hadin kai. Dalilin da ya sa haka shi ne domin hadin guiwa da ake yi tsakanin Sin da kasashen Afrika ba tare da wani sharadin siyasa ba, kuma bisa tushen girmama juna da moriyar juna, ka zalika hadin guiwar nan wani irin hadin guiwa ne da bangarori biyu ke samun nasara tare. (Halilu)