A kwanakin baya, mun gabatar da wani bincike a tsakanin masu sauraronmu dangane da 'me ka sani game da kasar Sin', kuma daga baya, mun sami sakonni da yawa daga masu sauraronmu. A yau kuma, bari mu karanto muku wani bayani da malam Mohammed Idi Gargajiga ya rubuto mana dangane da abubuwan da ya sani game da kasar Sin a fannoni daban daban, to, yanzu bari mu saurara yadda kasar Sin take a idonsa.
Malam Mohammed Idi Gargajiga ya ce, kasar Sin mai bin mulkin gurguzu, tana gabashin nahiyar Asia ne. A ran 1 ga watan oktoba na shekarar 1949 aka kafa jamhuriyar jama'ar Sin, birnin Beijing shi ne babban birnin kasar.
Kasar Sin tana da yawan mutane har kimanin biliyan 1.3 da kuma yawan kabilu 56, kuma manyan addinai da mutanen kasar Sin ke bi sune addinin Buddha, da addinin Dau,da addinin musulunci, da addinin kirista, da kuma Darikar katolika.
Kasar Sin tana aiwatar da manufar 'yancin bin addini, kowane dan kasa yana da 'yancin bin addini. Gwamnatin Sin kuma tana kiyaye masu bin addini da su yi harkokin addininsu yadda ya kamata.
Gwamnatin kasar Sin na aiwatar da manufar cin gashin kai a shiyyoyin kananan kabilu na kasarta. A ran 1 ga watan Yuli aka kaddamar da hanyar dogo ta Qinghai-Tibet da za ta bayar da muhimmiyar gudunmmawa ga karuwar tattalin arzikin jihar Tibet kuma za ta iya tabbatar da bunkasuwar tattalin arzikin jihar Tibet cikin hali mai dorewa.
kasar Sin tana da kujerar din din din a kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya, kuma har kullum kasar Sin tana tsayawa kan tafiyar da wata manufar harkokin waje ta zaman lafiya da rike mulkin kai ba tare da tsangwaman sauran kasashe ba. Bisa wannan manufa kasar Sin ta kulla huldar diplomasiyya tare da kasashe 165 na duniya.
A ran 3 ga wata, an kaddamar da tashar Internet ta gwamnati ta taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin kai a tsakanin Sin da Afrika da kuma taron ministocinsu a karo na 3, Tashar sunanta shine WWW. Focacsummit. Org, Domin kara zurfafa aminci na gargajiya da kara hadin kai a tsakanin Sin da Afrika mai taken Aminci da zaman lafiya da hadin kai da kuma samun bunkasuwa.
Ba shakka shugabannin kasar Sin suna yin babban kokari wajen dinke kasar Sin da kuma kara raya kasar don ta zama kasar gurguzu ta zamani. Ina iya tuna cewa a ran 1 ga watan Yuli na shekarar 1997 kasar Sin ta komo da shiyyar Hongkong karkashin babban yankin kasar ta, daga hanun kasar England sannan kuma ran 20 ga watan Disamba na shekarar 1999 kasar Sin ta komo da Macao da ke yammacin mashigin kogin Lu'u-Lu'u na kasar Sin karkashin mulkin gwamnatin jamhuriyar jama'ar Sin daga hanun kasar portugal.
Kamfanoni da masana'antu su ne kashin baya na tattalin arziki na kasar Sin, tun daga shekarar 1978 kasar Sin ta fara aiwatar da manufar bude kofa ga kasashen waje. Kuma kasar Sin ta yi nasara daga shekarar 1978-2003 kwatan kwacin yawan karuwar tattalin arzikin kasar Sin ya zarce kashi 9 cikin dari na wancan lokaci.
Bayan shekarar 1979 kasar Sin ta kebe shiyyoyin musamman na tattalin arziki guda biyar. A shekarar 1992 kasar Sin ta soma gabatar da manufar bunkasa tsarin tattalin arziki na kasuwanni.
A shekarar 2001 kasar Sin ta shiga cikin kungiyar ciniki ta duniya wato WTO. Ban da wannan kuma kasar Sin ta sami nasara wajen harba kumbo mai tafiye-tafiye a sararin sama mai daukar mutane kirar shenzhou 6. Kuma Birnin Beijing ya sami ikon shirya wasan Olimpic na yanayin zafi na shekarar 2008. Haka kuma wani kamfani da ke karkashin hukumar bincike na sararin samaniya ta kasar Sin ya fitar da watan dan adam zuwa kasar Nigeria.
A farkon shekarun 1990, gwamnatin kasar Sin ta fara yin amfani da fasaha wajen yin aikin noma da kare gonaki bisa gwaji, ta hanyar gudanar da ayyukan hadin guiwa a tsakanin kasa da kasa. Daga sakamakon gwajin da aka samu an gano cewa, ana samun sakamako mai kyau wajen yin amfani da irin wannan fasaha don kare gonaki da hana zaizayewar kasa, kazalika yawan kudi da aka kashe wajen yin aikin noma ya ragu da misalin kashi 20 cikin dari.
Ba shakka kasar Sin za ta iya kara samun babban sakamako cikin shekaru kadan masu zuwa, Sin za ta zama kasa mai karfin tattalin arziki a duk duniya.
Daga karshe ina mika sahihiyar godiya ga majalisar gudanarwa ta kasar Sin da duk jami'an gidan Rediyo CRI da ma'aikatansa baki daya musamman ma'aikatan sashenmu wato sashen Hausa na Radiyon kasar Sin. Domin ta hanyar sauraron CRI ne nake iya samun labarun gaskiya da suke faruwa a kasar Sin da ma na sauran kasashen duniya.
Gaskiya masaniyar malam Mohammed Idi Gargajiga dangane da kasar Sin ta burge mu kwarai, kuma daga abubuwan da ya rubuta mun gane zumuncin da ke cikin zuciyarsa ga kasar Sin da jama'arta. Mun gode, kuma Allah ya kara dankon zumunci a tsakanin jama'ar Sin da ta Afirka. (Lubabatu)
|