Ran 26 ga watan Oktoba, a nan Beijing aka rufe cikakken taro na karo a 7 na kwamitin kula da taron wasannin Olympic na lokacin zafi a karo na 29 na Kwamitin Wasannin Olympic na Duniya wato IOC. A gun taron manema labaru da aka yi bayan taron, shugaban kwamitin kula da taron wasannin Olympic na lokacin zafi na karo na 29 Hein Verbruggen yana ganin cewa, yanzu ana shirya taron wasannin Olympic na shekarar 2008 na Beijing lami lafiya bisa shirin da aka tsara, banganren birnin Beijing yana cika alkawarin da ya yi a lokacin neman samun damar shirya wannan taron wasannin Olympic. Ya kuma yi imanin cewa, bisa ci gaban da yake samu a yanzu, birnin Beijing zai iya share fage daga dukan fannoni kafin a bude taron wasannin Olympic a shekarar 2008.
Ran 24 ga watan Oktoba, a nan Beijing, bayan da ya ziyarci filin wasan kasar Sin da cibiyar wasan iyo ta kasar Sin, shugaban kwamitin IOC Jacques Rogge ya yi babban yabo kan wadannan filayen wasa 2 da za a yi amfani da su a gun taron wasannin Olympic na Beijing, ya kuma mayar da su a matsayin nagartattun gine-gine na duniya, kamar yadda dakin wasan kwaikwayo na Sydney yake.
Ran 26 ga watan Oktoba, a nan Beijing, Mr. Hein Verbruggen ya fayyace cewa, za a sayar da tikitocin taron wasannin Olympic na Beijing da yawansu ya kai misalin kashi 80 cikin dari a kasar Sin. Da yawa daga cikin wadannan tikiti ne za a sayar da su cikin araha, don bayar da dama ga mutane masu yawa su iya kallon gasanni a filayen wasa kai tsaye.
Ran 26 ga watan Oktoba, a nan Beijing, kwamitin IOC ya ba da wata sanarwar cewa, kwamitin gudanarwar na kwamitin IOC ya zartas da kuduri kan ajandar gasanni ta taron wasannin Olympic na shekarar 2008 na Beijing. Ba kamar yadda aka yi a da ba, za a yi karon karshe na gasannin iyo da na gasanin wasan lankwashe jiki tsakanin kungiyoyi da na gasar wasan lankwashe jiki ta mutum guda ta duk fannoni da na eurythmics da kuma na gudun Marathon a safe. Da yamma da dare kuma za a yi karon karshe na gasar tsinduma cikin ruwa da na gasar salon-iyo da na wasan kwallon ruwa wato water Polo da kuma karon karshe na gasannin lankwashe jiki iri daban daban da kuma sauran gasannin wasan guje-guje da tsalle-tsalle.
Ran 26 ga watan Oktoba, a nan Beijing, mataimakin shugaban gudanarwa na kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing Jiang Xiaoyu ya bayyana cewa, tun bayan da aka fara daukar masu sa kai domin taron wasannin Olympic na Beijing na shekarar 2008 da na nakasassu a watan Agusta na shekarar bana har zuwa yanzu, mutane suna alla-alla da zama masu sa kai. Yanzu yawan wadannan masu sa kai da suka yi rajista ya wuce 220,000.(Tasallah)
|