Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-01 18:41:27    
Mr. Dujkovic ya fara horas da kungiyar wasan kwallon kafa ta Olympic ta kasar Sin

cri

Ran 21 ga watan Oktoba, a gun taron manema labaru da aka yi a nan Beijing, Hadaddiyar Kungiyar Wasan Kwallon Kafa ta kasar Sin wato CFA ta sanar da cewa, Mr. Ratomir Dujkovic dan kasar Serbia ya zama babban malamin horas da wasanni na kungiyar wasan kwallon kafa ta Olympic ta kasar Sin. Bisa yarjejeniyar da kungiyar CFA da Mr. Dujkovic suka rattaba hannu a kai, an ce, Mr. Dujkovic zai shugabanci kungiyar kasar Sin da ta shiga gasannin wasan kwallon kafa na taron wasannin Olympic da za a yi a nan Beijing a shekarar 2008, kuma za ta yi kokarin shiga cikin nagartattun kungiyoyi 4. Wa'adin aikinsa zai cika a watan Satumba na shekarar 2008.

Ko da yake ba a iya kwatanta gasar wasan kwallon kafa ta taron wasannin Olympic da gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa ba, amma samun lambar zinare a gun taron wasannin Olympic wani babban yabo ne. Shi ya sa hadaddun kungiyoyin wasan kwallon kafa na kasashe da yankuna masu yawa suka dora muhimmanci kan wannan gasa sosai. A matsayin kasa mai masaukin taron wasannin Olympic na Beijing, masu kishin wasan kwallon kafa na kasar Sin suna fatan kungiyar wasan kwallon kafa ta Olympic ta kasar Sin za ta sami maki mai kyau a gun taron wasannin Olympic na Beijing. A cikin irin wannan hali ne, kungiyar CFA ta tsai da kudurin nada dan kasashen waje da ya horas da kungiyar wasan kwallon kafa ta Olympic ta kasar Sin. Ta yi rabin shekara tana dudduba da kuma zabi malami mai horas da wasanni. A karshe dai ta zabi Mr. Dujkovic. A gun gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa ta shekarar 2006 da aka yi a kasar Jamus, Mr. Dujkovic shi na mai horas da wasanni na kungiyar kasar Ghana, wadda a karo ne farko da ta shiga gasar cin kofin duniya, a karshe dai, kungiyar kasar Ghana ta zama kasar Afirka ce kurum da ta shiga cikin nagartattun kungiyoyi 16. A sakamakon haka ne, Mr. Dujkovic ya fara shahara a duk duniya. Bayan wannan gasar, Mr. Dujkovic ya kammala aikinsa a kasar Ghana.

A gun taron manema labaru da aka yi a ran 21 ga watan Oktoba, Mr. Dujkovic ya bayyana cewa, zai yi iyakacin kokari don shugabantar kungiyar kasar Sin da ta shiga kungiyoyi masu nagarta guda 4 a gun gasar wasan kwallon kafa ta maza ta taron wasannin Olympic na shekarar 2008 na Beijing.

A gaban manema labaru na kasar Sin, Mr. Dujkovic mai cike da imani ya yi bayani cikin tawali'u cewa,'Da farko dai zan gaya muku cewa, ban gwanance wajen yin surutu ba, amma na fi gwada gwaninta a filin wasan kwallon kafa. Ina fari ciki sosai saboada zama malami mai horas da wasanni na kungiyar kasar Sin.'

Saboda yana kasancewa da babban gibi a tsakanin kungiyar kasar Sin da kungiyoyin kasashen duniya masu karfi, shi ya sa an mayar da jagorancin kungiyar kasar Sin wajen shiga ciki nagartattun kungiyoyi 4 a gun gasar wasan kwallon kafa ta taron wasannin Olympic na Beijing tamkar aiki ne mai matukar wuya. Game da wannan kuma, Mr. Dujkovic ya ce,'Mai yiwuwa ne dukan Sinawa suna fatan samun maki mai kyau a gun taron wasannin Olympic, a gaskiya kuma da wuya ne kungiyar kasar Sin za ta iya shiga cikin nagartattun kungiyoyi 4, duk da haka yanzu kungiyar wasan kwallon kafa ta kasar Sin ta zama ta 103 a duk duniya, kungiyar kasar Ghana kuma tana cikin nagartattun kungiyoyi 30 a duniya, amma makasudina shi ne shugabantar kungiyar kasar Sin wajen shiga cikin nagatattun kungiyoyi 4 a gun taron wasannin Olympic. Da can kungiyoyin da ke karkashin shugabancina sun taba samun ci gaba, shi ya sa na yi imanin cewa, kungiyar kasar Sin za ta sami maki mai kyau a gun taron wasannin Olympic na Beijing.'

Ban da wannan kuma, Mr. Dujkovic ya yi karin haske kan ra'ayinsa kan aikin horas da wasanni, ya ce,'Ra'ayina kan wasan kwallon kafa shi ne kara kai hari, ina fatan kungiyar da ke karkashin shugabancina za ta kara kai hari, za ta kyautata saurin wasa, 'yan wasan za su gaggauta ba da kwallo a tsakaninsu.'

Wani jami'in kungiyar CFA ya yi bayani kan dalilin da ya sa aka zabi Mr. Dujkovic inda ya ce shi ne domin a karkashin shugabancinsa, kungiyoyin kasashen da ba su kan gaba a fannin wasan kwallon kafa sun sami babban ci gaba. shi ya sa kungiyar CFA take fatan cewa, kamar yadda ya yi a da, Mr. Dujkovic zai taimaki kungiyar wasan kwallon kafa ta Olympic ta kasar Sin da ta sami babban ci gaba a cikin gajeren lokaci.

Jama'a masu sauraro, za mu zura ido kan ko kungiyar wasan kwallon kafa ta Olympic ta kasar Sin da ke karkashin shugabacin Mr. Dujkovic za ta ci nasara a gun taron wasannin Olympic na Beijing ko a'a.(Tasallah)