Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-01 17:19:42    
Mr. Hu Jintao ya yi shawarwari da shugaban kasar Guinea-Bissau

cri

Ran 1 ga wata a nan birnin Beijing, Mr. Hu Jintao, shugaban kasar Sin ya yi shawarwari da Mr. Joao Bernardo Vieira, shugaban kasar Guinea-Bissau, wanda ya kawo ziyarar aiki a nan kasar Sin, da kuma hallartar taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan harkokin hadin kai a tsakanin Sin da Afrika. Inda bangarorin biyu suka samu muhimmin ra'ayi daya kan inganta dangantakar da ke tsakanin bangarorin biyu ta zaman karko a cikin dogon lokaci, da ta hadin kai a duk fannoni.

Shugabannin kasashen biyu sun bayyana cewa, za su yi kokari domin tabbatar da samu nasarar taron koli na Beijing, kuma gaba daya suka bayyana cewa, suna fatan habaka hadin kansu a fannonin sha'anin su, da sha'anin noma, da raya manyan ayyukan kasa, da kuma kara yin shawarwari da hadin kai a cikin harkokin kasashen duniya.

Mr. Hu Jintao ya jaddada cewa, ya kamata kasashen biyu su tsaya kan manufar samu moriyar juna, da samu bunkasuwa tare, su mai da hankali sosai kan ayyukan hadin kai da suke yi wajen tattalin arziki da ciniki, da sa himma domin neman sabbin fannoni da hanyoyi na hadin kansu na samun moriyar juna; da kuma karfafa hadin kansu a cikin muhimman tsare-tsaren taron dandalin tattaunawa kan harkokin hadin kai a tsakanin Sin da Afrika, da kara yin shawarwari kan bunkasuwar taron dandalin tattaunawa nan gaba, da aiwatar da ayyukan nan gaba na taron, da kuma karfafa hadin kansu a fannonin horar da kwararru, da karfinsu, da dai sauransu.

Mr. Vieira ya ce, jama'ar kasar Sin sun ba da taimako sosai ga kasar Guinea-Bissau a fannonin sha'anin noma, da raya manyan ayyukan kasa, da kuma sha'anin kudi. Ya jaddada cewa, kasar Guinea-Bissau za ta ci gaba da tsayawa kan manufar Sin daya tak. (Bilkisu)