Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-11-01 11:50:05    
An fara taron manyan jami'an kasar Sin da kasashen Afirka na 5

cri

A ran 1 ga wata da safe, agogon Beijing, an fara taron manyan jami'an dandalin tattaunawa kan hadin guiwar kasar Sin da kasashen Afirka a karo na biyar a nan birnin Beijing. Wakilai na kasar Sin da na dukkan kasashe 48 na membobin dandalin suke halartar wannan taro.

Mr. Zhai Jun, babban sakataren kula da harkokin shirya taron koli na dandali kuma mai ba da taimako ga ministan harkokin waje na kasar Sin da Mr. Haile Kiros, jakadan kasar Habasha da ke nan kasar Sin kuma manzon musamman na gwamnatin kasar Habasha wadda ke shugabantar dandalin tattaunawa kan hadin guiwar kasar Sin da kasashen Afirka tare da kasar Sin sun bayar da jawabai daya bayan daya a gun bikin kaddamar da taron manyan jami'ai.

Mr. Zhai Jun ya ce, shekarar bana shekara ce ta cikon shekaru 50 da kafuwar dangantakar diplomasiyya a tsakanin Jamhuriyar Jama'ar Sin da kasashen Afirka. A wannan muhimmiyar shekara, tabbas ne taron koli da za a yi zai kai alakar dangantakar da ke tsakanin Sin da kasashen Afirka zuwa wani sabon mataki, kuma zai bayar da gudunmmawa kan yadda za a raya hadin guiwa da gama kai a tsakanin kasashe masu tasowa, sannan kuma zai raya harkokin shimfida zaman lafiya da neman bunkasuwa a duniya baki daya.

A cikin nasa jawabi, Mr. Kiros ya ce, ana raya dangantakar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka ne bisa tushen sada zumunta da yin hadin guiwa da neman bunkasuwa tare. Bayan taron ministoci na biyu na dandalin tattaunawa kan hadin guiwar kasar Sin da kasashen Afirka da aka yi a kasar Habasha, aikace-aikacen da bangarorin Sin da kasashen Afirka suke yi a fannonin cinikayya da horar da kwararru da neman bunkasuwar aikin gona da al'adu da yawon shakatawa da jiyya da dai sauransu suna ta samun cigaba yadda ya kamata. Hadin guiwar moriyar juna a tsakaninsu ma tana ta samun cigaba. Tabbas ne, taron koli da za a yi a tsakanin shugabannin kasar Sin da kasashen Afirka zai kara ciyar da alakar hadin guiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka gaba tare da samun bunkasuwa tare.

Taron manyan jami'ai da za a shafe kwanaki 2 ana yinsa, muhimmin taro ne ga dandalin tattaunawa kan hadin guiwar kasar Sin da kasashen Afirka. A gun wannan taro, za a dudduba takardun da aka shirya don taron koli na Beijing, kuma za a share fage na karshe ga taron koli na farko da taron ministoci na uku na dandalin tattaunawa kan hadin guiwar kasar Sin da kasashen Afirka. (Sanusi Chen)