Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-31 19:26:26    
Ziyara a Kenya kyakkyawan shakatawa ne

cri

Tun bayan da kasar Kenya da ke gabashin Afirka ta zama wurin shakatawa da Sinawa suka iya kai mata ziyara a shekarar 2004 har zuwa yanzu, Sinawa sun kara kai wa wannan kyakkyawar kasa ziyara. A cikin lokacin hutu don taya murnar ranar cikon shekaru 57 da kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin, daruruwan masu yawon shakatawa na kasar Sin sun je kasar Kenya sun fahimci halin musamman da wannan babban fili mai ciyayi na Afirka ke nunawa. Bayan da suka kai ziyara ga shahararrun wuraren shakatawa na kasar Kenya, kamar su hotel na Treetop da Nakuru da shiyyar kiyaye halitta ta Masai Mara, sun fahimci halin musamman na bakar Afirka da kansu, har ma sun ji dadin kallon namun daji iri daban daban a kusa da su.

Bisa kididdigar da aka yi, an ce, a cikin shekarun nan da suka wuce, yawan masu yawon shakatawa na kasar Sin yana karuwa cikin sauri. Mr. Han Jun, wanda ya yi shekaru da dama yana tafiyar da wani kamfanin yawon shakatwa a kasar Kenya, ya bayyana cewa, 'Sinawa sun kara kai wa kasar Kenya ziyara a cikin shekarun baya da suka shige. Mutanen Sin fiye da 4,000 sun je kasar Kenya a shekarar 2004, a shekara 2005 kuma yawansu ya zarce 10,000. A wannan shekarar kuwa, a ganinmu, ko shakka babu wannan adadi zai wuce 20,000'. A matsayin wurin shakatawa ga Sinawa, ina tsammanin cewa, kasar Kenya yana fuskantar makoma mai kyau wajen samun ci gaba.'

Game da dalilin da ya sa ta kai wa kasar Kenya ziyara, Shen Chenxia, 'yar birnin Beijing ta bayyana cewa, 'Saboda Afirka wuri ne mai ban mamaki a gare mu. Dalilin da ya sa na yi yawon shakatawa a kasar Kenya shi ne domin kasar Kenya ainihin kasar Afirka ce da ta nuna halin musamman iri na Afirka. Da can ban san Afirka sosai ba, amma na gano abubuwa masu ban mamaki da yawa a nan. Ban taba tabo namun daji a kusa da su hakan ba, sa'an nan kuma, suna zama tare da mutane lami lafiya a cikin shiyya mai girma hakan.'

Wata malama mai suna Xiang Ling ta taba yin yawon shakatawa a kasar Australia da wasu kasashen Turai da Kudu maso Gabashin Asiya, ta bayyana cewa, kasar Kenya tana nuna halin musamman nata, in an kwatanta ta da sauran kasashen da ta taba ziyara. Ta ce, 'A ganina, kallon namun daji cikin mota yana da kyau sosai. ya jawo hankalina sosai. Ban da wannan kuma, wurare masu ni'ima da ke kan babban fili mai ciyayi suna da kyaun gani. Shiyyar kare halitta ta Masai Mara gidan gaskiya ne ga dabbobi, kuma gida ne ga mutane a zukatammu. Na ji sakin jiki a nan, mutane da dabbobi suna zama tare cikin jituwa.'

Ba babban fili mai ciyayi na Afirka da namun daji kawai suka jawo hankulan mutane ba, har ma masu yawon shakatawa na kasar Sin sun cika jakunkunansu da kayayyakin hannu masu nuna halin musamman na kabilu na kasar Kenya.