Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-31 16:09:01    
Neman fatan alheri tare da jama'ar kasashen Afirka

cri

A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, masana'antu masu dimbin yawa sun je kasashen Afirka domin zuba jari ko yin kasuwanci. Yanzu, idan ka yi yawo a kan titunan biranen kasashen Afirka, ka kan ga wasu Sinawa. To, mene ne gudunmmawar da masana'antun kasar Sin suke bayarwa a kasashen Afirka? A idanun jama'ar Afirka, yaya kayayyakin da aka shigar da su daga kasar Sin? Yanzu, ga wani rahoton da wakilinmu Bello Wang da ke birnin Lagos na kasar Nijeriya ne ya aiko mana.

Mutanen kasar Nijeriya sun sani, babbar kasuwar Lagos, kasuwa ce mafi girma a kasar Nijeriya inda ake sayar da kananan kayayyakin masarufi iri iri ciki har da kyale da tufafi da kananan injuna iri iri. A wurin da fadinsa ya kai murabba'in kilomita 2, akwai kantuna fiye da dubu 10. A kowace rana, 'yan kasuwa da masu sayen kayayyaki suna ribibin saye da sayar da kayayyaki a wannan kasuwa. Wasu kayayyaki daga cikinsu kayayyaki ne da aka shigar da su daga kasar Sin. Mr. Olawale, wani direkta ne da ke kula da aikin sayar da tufafi a cikin wani kamfanin sayar da tufafin kasar Sin da ke kasar Nijeriya. Ya gaya wa wakilinmu cewa, "Kamfanonin kasar Sin suna samar mana da guraban aikin yi da yawa. 'Yan kasuwa namu suna samu kayayyakin kasar Sin a kasarmu, ba dole ba ne ya tafi kasashen waje domin neman kayayyakin kasashen waje. Bugu da kari kuma, bayan shigowar kayayyakin kasar Sin a kasar Nijeriya, matsakacin farashin kayayyaki ya samu raguwa sosai. Sakamakon haka, mutane masu karamin karfi suna iya sayen kayayyakin masarufi da yawa da suke bukata."

Yanzu, yawancin 'yan kasuwa na kasar Sin suna sayar da kayayyakin masarufi kawai a kasar Nijeriya. A waje daya kuma, wasu manyan masana'antu da kamfanoni na kasar Sin suna zuba jari a kasar Nijeriya kan ayyukan shimfida hanyar dogo da hanyoyin mota da haka rijiyoyi da aikin gona da ayyukan samar da wutar lantarki da sadarwa da dai sauransu. Jama'ar wurin suna jin dadin wannan ayyukan yau da kullum. Kamfanin CCECC ya dade yana zuba jari a kasar Nijeriya. A cikin shekaru da yawa da suka wuce, ya kammala ayyukan shimfida hanyar dogo da hanyoyin mota da yawa a kasar. Lokacin da yake zantawa kan ayyukan da kamfanin ya yi, Mr. Zhou Tianxiang, babban direktan kamfanin CCECC da ke kasar Nijeriya ya ce, "Yawancin ma'aikata, ciki har da wasu direktocin kamfaninmu mutanen Nijeriya ne. Idan wani Basine ya zo, dole mu dauki mutanen wuri a kalla 10."

Kamfanin CGCOC, kamfanin kasar Sin daban ne da ya dade yake zuba jari a kasar Nijeriya. Ya zuwa yanzu, wannan kamfani ya riga ya haka rijiyoyi fiye da dubu 10. Bugu da kari kuma, yanzu ba ma kawai wannan kamfani yana ci gaba da neman kwangiloli ba, har ma yana raya gangun noma a kasar Nijeriya.

Jama'ar kasar Nijeriya suna yaba wa ayyukan da kamfanonin kasar Sin suka yi da hadin guiwar da ake yi a tsakanin Sin da kasar Nijeriya. Lokacin da yake zantawa kan hadin guiwar da ake yi a tsakanin Sin da kasar Nijeriya kan aikin gona, malam Salisu Dawanau, wani ma'aikaci ne da ke aiki a kamfanin buga kudin Nijeriya, ya ce, "Shigowar alakar kasar Sin yanzu, an iya samun hanyar noma mafi sauki, an iya samun takin zamani masu inganci da ainihin dabarun noma masu inganci daga kasar Sin. Hakika mutane sun amfana kuma suna fatan wannan alakar dangantaka da kuma abuta za ta ci gaba."

Malam Bello, wani dan wasan kwallon kafa ne na kulab na kwallon kafa na hukumar kula da harkokin tashar ruwa ta kasar Nijeriya ya bayyana cewa, "Akwai mutanen China da kamfanonin China daban-daban suna cikin kasar Nijeriya. Ai ka ga zuwan wadannan mutanen China sun waya mana ido, sun nuna mana ainihin abin da duniya ke ciki. Ka ga shigowarsu wani alheri ne, wani kamar kyauta ne da Allah ya kawo wa Nijeriya. Mu ma sai mu yi kokari mu ba su hadin guiwa, mu ba su goyon baya domin su ci gaba, mu ma mu samu ci gaba." (Sanusi Chen)