Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-30 17:26:43    
Kabilar Dai

cri

An fi samun 'yan kabilar Dai a cikin yankin Xishuangbanna na kabilar Dai da gundumar Dehong ta kabilun Dai da Jingpo masu cin gashin kai da ke jihar Yunnan ta kasar Sin, wasu kuwa suna da zama a cikin gundumomi fiye da 30 na jihar Yunnan. Bisa kidayar yawan mutanen kasar Sin a karo na biyar da aka yi a cikin shekara ta 2000, yawan 'yan kabilar Dai ya kai fiye da miliyan 1.1. 'Yan kabilar Dai suna yin amfani da harshen kabilar Dai, kuma kabilar tana da harafinta. A tsakiyar karni na 20, an yi gyare-gyare kan harafin kabilar.

 

Bayan kafuwar kasar Sin a cikin shekara ta 1949, 'yan kabilar Dai sun samun 'yancin gudanar da harkokinsu da kansu. A cikin shekara ta 1953, an kafa yankin Xishuangbanna mai cin gashin kai na jihar Yunnan. Daga baya kuma an yi gyare-gyare kan gonaki da tsarin zamantakewar al'umma, sabo da haka 'yan kabilar Dai sun bi hanyar gurguzu, kuma tattalin arziki da al'adun gargajiya na kabilar sun samu gagarumin ci gaba. A cikin shekaru fiye da 50 da suka gabata, an raya ayyukan ban ruwa sosai da karfafa muhimman ayyuka na gonaki da kuma ingiza fasahohin noma na zamani, sabo da haka yawan amfanin gona ya samu karuwa sosai. bugu da kari kuma masana'antu na birane da kauyuka na kabilar sun samu bunkasuwa kwarai da gaske, daya bayan daya ne an kafa kamfanonin haka ma'adinai da samar da wutar lantarki da sarrafa abinci da dai sauransu. Kafin tsakiyar karnin da ya gabata, ba a iya samu wata hanyar motoci ko daya a cikin yankin 'yan kabilar Dai ba, amma yanzu yawancin kauyuka sun gina hanyoyin motoci. Game da sha'anin ilmi, an kafa makarantun firamare masu yawa a wurare daban daban, ban da wannan kuma an kafa makarantun sakandare da na koyar da sana'o'i bi da bi, haka kuma a cikin makarantu da yawa an yi ayyukan koyarwa da harshen kabilar Dai. A yankin Xishangbanna da Dehong kuwa ana bugawa jaridu da harafin kabilar Dai, suna watsa labarai da harshen Dai, kuma ana fassara da buga littattafai iri daban daban daga Sinanci zuwa harshen Dai.