Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-30 10:55:40    
Afirka ta Kudu tana sa ran alheri kan taron koli na Beijing na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka

cri
Ran 29 ga wata, a birnin Johannesburg, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Afirka ta Kudu Ronnie Mamoepa ya sanar da cewa, a ran 3 ga watan Nuwamba, shugaban kasar Thabo Mvuyelwa Mbeki zai shugabanci tawagar manyan jami'an gwamnatin kasar zuwa Beijing, don halartar taron koli na Beijing na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka da za a yi tun daga ran 4 zuwa ran 5 ga watan Nuwamba, gwamnatin kasar tana sa ran alheri kan wannan taron koli.

Mr. Mamoepa ya bayyana cewa, taron koli na Beijing dandali ne da kasashen Sin da Afirka suke tattaunawa da hadin gwiwa a tsakaninsu don neman samun bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'ummar kasa. Ya kara da cewa, gwamnatin kasar Afirka ta Kudu za ta tattauna tare da shugabannin kasashen Sin da Afirka kan matakai da manufar yin hadin gwiwa da za ta bi wajen aiwatar da sabon shirin abokai kan bunkasa Afirka a gun taron koli nan.(Tasallah)