Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-27 17:28:38    
Jami'an kasashen Afirka suna sa ran alheri kan taron koli na Beijing na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka

cri

Lokacin da suke zantawa da wakilan kamfanin dillancin labaru na Xinhua na kasar Sin a kwanan baya, ministan harkokin waje da yin hadin gwiwa da kasashen waje na kasar Guinea Mamady Condé da ministan ciniki da bunkasuwar masana'antu da kuma kula da sabon shirin abokai kan bunkasa Afirka Paul Biyoghe Mba da ministan harkokin waje da yin hadin gwiwa na kasar Mauritania Ahmed Ould Sid' Ahmed dukansu suna sa ran alhari kan taron koli na Beijing na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka.

Mr. Condé ya bayyana cewa, kasar Guinea da sauran kasashen Afirka suna fatan karfafa huldar abokantaka da hadin gwiwa da ke tsakanin bangarorin Sin da Afirka ta hanyar taron koli na Beijing na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka da za a yi ba da dadewa ba. Kasashen Afirka suna fatan kasar Sin za ta kara taka rawa a fannonin magance barkewar rikici a yankin Afirka da kuma ingiza bunkasa kasashen Afirka bai daya ta hanyar kara hada kanta da Kungiyar Tarayyar Afirka. Yana kuma ganin cewa, bunkasuwar kasar Sin wata dama ce ga kasashen Afirka, ba barazana ba ce. Kasar Sin tana taimakon kasashen Afirka cikin sahihanci, kuma ba tare da sharadin siyasa ba. Ban da wannan kuma, kasashen Afirka za su iya koyon tsarin bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin.

Mr. Mba ya ce, kasashen Afirka da Sin suna inganta huldar da ke tsakaninsu. Kasar Sin tana taimakon kasashen Afirka da yawa, tana zuba jari zuwa ga kasashen Afirka da yawa. Kamfanonin kasar Sin sun yi ayyuka masu yawa a Afirka, kamar su shimfida hanyoyin mota da gadoji da gina filayen wasa da gine-gine. Kasar Sin abokiya ce da kasashen Afirka suke gaskatawa.

Mr. Ahmed ya yi bayanin cewa, taron koli na Beijing na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da Afirka da za a yi ba da dadewa ba zai kafa dangantakar abokantaka ta muhimman tsare-tsare ta sabon salo a tsakanin Sin da Afirka, irin wannan dangantaka ta bayyana burin dukan bangarorin Sin da Afirka, ita kuma tsari ne na yin tattaunawa da hadin gwiwa da bangarorin 2 suka kafa don fuskantar kalubalen neman samun ci gaba tare.(Tasallah)