Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-26 15:34:25    
Ana ta kara sada zumunci a tsakanin kasashen Sin da Morocco

cri
kasar Morocco tana arewa maso yammacin babban yankin Afrika. Ita ce kuma kasar Afrika ta biyu da ta kulla huldar diplomasiya da kasar Sin, bayan da aka kafa sabuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin. A lokacin da shugabannin Sin da kasashen Afrika za su kira taron dandalin hadin kan Sin da Afrika a nan birnin Beijing, wakilanmu sun kai ziyara ga Mr. Cheng Tao, jakadar kasar Sin da ke kasar Morocco kan kyakkyawar dangantakar hadin kai da ke tsakanin Sin da Morocco. Yanzu ga cikakken bayanin da wakilanmu suka ruwaito mana daga birnin Rabat.

Da farko, Mr. Cheng Tao ya yi bayani kan tarihin kyakkyawar dangantakar da ke tsakanin Sin da Morocco. Ya ce,"Ya kasance da dogon tarihin yin cudanya, da kyakkyawar abokantakar gargajiya a tsakanin jama'ar kasashen Sin da Morocco. Tun daga tsakiyar karni na 7, wani mutum mai suna Du Huan na daular Tang na kasar Sin ya taba zuwa Morocco. Wani babban mai sha'awar yawon shakatawa na kasar Morocco kuma ya taba zo kasar Sin a shekarar 1346. An mika al'barushi da dabarar dab'i na kasar Sin ta hanyar siliki zuwa kasar Morocco daga kasar Masar, bayan haka kuma an ci gaba da mika musu zuwa Turai daga mashigin tekun Gibraltar, wannan ya zama wani labari mai kyau da aka yadawa a kasar Morocco."

A shekarar 1958, kasashen Morocco da Sin sun kulla huldar diplomassiya. Bambancin da ke kasancewa a tsakaninsu wajen tsarin zaman al'umma bai hana kara bunkasuwar kyakkyawar dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu ba. Mr. Cheng yana ganin cewa, manufofi 5 na zama tare cikin lumana da kasar Sin ke tsayawa a kai, su ne muhimmin dalili daya ne. Ya ce,"A cikin shekaru 48 da suka wuce, mun bunkasa dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu bisa tushen nuna girmamawa da juna, da amincewa da juna, da zaman daidaitawa, da kuma samu moriyar juna, ana bunkasuwar dangantakar kamar yadda ya kamata. Bangarorin biyu sun samu sakamako mai kyau wajen hadin kai a fannoni daban daban."

Mr. Cheng ya gaya wa wakilanmu cewa, kasashen Morocco da Sin sun taba gamuwa da harin da aka kai musu, kuma suna fuskantar nauyin bunkasa tattalin arziki, sabo da haka suna da ra'ayi daya a fannoni daban daban. Kasar Sin tana daukar ra'ayin sauke nauyin da ke bisa wuyanta, da kuma mai adalci, wannan kuma ya sa kasar Morocco ta kara amincewa da kasar Sin. Da zuciya daya ne kasar Morocco take fatan kasar Sin za ta kara samun bunkasuwa a kwana a tashi, kuma tana fatan za ta yi koyon fasahohin da kasar Sin ta samu a yunkurin raya kasar, da kuma kara hadin kansu da samun moriyar juna a tsakanin Morocco da Sin.

Mr. Cheng ya bayyana cewa, a cikin 'yan shekarun da suka wuce, dangantakar da ke tsakanin Sin da Morocco wajen tattalin arziki da ciniki ta samu ci gaba sosai, jimlar kudi na ciniki a tsakanin bangarorin biyu ta karu da 30 cikin dari a ko wace shekara. Mutanen kasar Morocco suna maraba da kyakkyawan ciniki na kasar Sin masu kyau da kuma araha.

Bayan haka kuma, kasashen Sin da Morocco sun hada kansu a fannonin sha'anin sa, da sana'ar yawon shakatawa, da dai sauransu kamar yadda ya kamata.

Kan taron koli na dandalin hadin kan Sin da Afrika da za a shirya a birnin Beijing, Mr. Cheng ya ce,"Bangaren Morocco yana mai da hankali sosai kan taron koli na Beijing, da taron ministoci na dandalin hadin kan Sin da Afrika, kuma ya gabatar da shawarwari masu kyau kan wannan taro. Yana ganin cewa, wannan ne wata dama mai kyau ga shugabannin kasar Sin da kasashen Afrika da su kara fahimtar juna, da musaya ra'ayoyinsu, da kuma sami hakikanin ra'ayi daya."

Mr. Cheng yana cike da imani cewa, ta kokarin da bangarorin biyu suke yi, kyakkyawar dangantakar hadin kai da ke tsakanin kasashen biyu za su sami ci gaba, kuma za ta kai wani sabon matsayi. (Bilkisu)