Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-10-25 19:45:07    
Yadda kasar Sin take a idon masu sauraronmu(1)

cri

A kwanakin baya, mun gabatar da wani bincike a tsakanin masu sauraronmu dangane da 'me ka sani game da kasar Sin', kuma daga baya, mun sami sakonni da yawa daga masu sauraronmu. Yanzu za mu karanto muku wani bayanin da malam Salisu Muhammad Dawanau mazaunin birnin Abuja na tarayyar Nijeriya ya rubuto mana dangane da abubuwan da ya sani game da kasar Sin a fannoni daban daban, wanda kuma ke da lakabin 'son kowa kin wanda ya rasa'.

malam Salisu Muhammad Dawanau daga birnin Abuja na tarayyar Nijeriya ya rubuto mana cewa, 'bigi sai bigi, babba sai babba', yadda masu hikimar magana su kan ce ke nan a lokacin da suka ga abu mai girma wanda bai da iyaka.

A wannan duniya tamu, a yau, babu kasar da take da yawan jama'a kamar kasar Sin. Amma duk da wannan yawa ita ce take ciyar da kanta ba tare da neman agaji daga kasashen yammaci ko na Turai ba.

Hakika?wannan kwazo da jarumtaka da juriya da hangen nesa da kuma kishin kasa da shugabannin kasar ke da shi a zukatansu ya taimaka wa kasar don cimma bakatunta masu muhimmanci da kuma inganci.

Sinawa mutane ne masu kawaici da karimci da tawali'u, da kuma sanin ya kamata. Na ga hakan a fili yayin da na ziyarci kasar Sin. Sinawa mutane ne masu kishin asalinsu a duk inda suke. Ina kyautata zaton wannan dabi'a ya samo asali ne daga irin horo da da'a da kuma koyarwar shugabanni da kuma iyaye na gari, hakika na kan yaba musu. Idan akidar kasa da na masu mulkin kasar tana da kyau, to dole ne al'umar kasa ta ginu bisa kyakkyawar akida da kuma samun alkibla mafi armashi ta yadda zata zama abin koyi.

Rayuwar Sinawa ta kara ingantuwa kwarai, musamman tun daga shekaru 25 ? 30 can baya. An samu gagarumar ci gaba ta fannin tsarin rayuwa da na walwala da kuma zamantakewa. Haka nan, yalwatar arziki ya karu sosai a yau. A da can baya, kalmar da ke bakunan Sinawa, a kasar Sin, ita ce "ko ka ci abinci"? saboda tsadar rayuwa, amma a yanzu wannan kalmar ta canza zuwa "ko nawa ka ci riba"? don mutane sun samu abinci da kudin sayen abinci, rayuwa ta canza har ma suna yin ajiya da zuba jari da kuma yin kasuwanci. Jama'a sai walwala ake yi a kullum.

Hanyoyin sufuri da ilimi da tarbiya da noma da shari'a da kiwon lafiya da kimiyya da fasaha da tsarin iyali mai dacewa (da sauransu) duk sun gyaru bisa dacewa da wannan zamani.

Wayewar kai, abu ne mai muhimmanci musamman ta hanyar fahimtar zamani da kuma ci gaban kasa da al'ummarta. A zahiri, kasar Sin tana da tarihi mai tsawon gaske. Sau da yawa, mutane kan gwada ko kimanta inganci da kuma ilmin al'umma ta fannin lokacin da kasa ko al'ummarta kansu ya waye. A nan, ina so mu sani cewar, kasar Sin kanta da na al'ummarta a waye suke, don kasar Sin tana da tarihin wayewar kai na fiye da shekaru kimanin 4,000 da suka shude.

A shekara ta 1990, kasar Sin ta kashe kudade masu dumbin yawa wajen gyaran wuraren tarihi, da kare wadannan wurare, kuma ta yi nasara bisa wannan aiki. Hakika, wuraren tarihi da na al'adun kasar Sin sun yi fice a Duniya. Kasar tana yin gyare-gyare, akai-akai, sabo da kar 'yan baya su mance asalinsu, kuma don tarihi ya ci gaba. Saboda haka ne UNESCO (ta Majalisar Dinkin Duniya) ta sanya wurare 28 na kasar a cikin jerin wuraren tarihi da al'adu na Duniya wadanda ba za a mance da su ba. Masu yawon bude ido daga kasashen Duniya daban-daban suna ziyartar kasar Sin kowace shekara. Misali, wurare irin su Babbar Ganuwa da Beihai Park da Dandalin Tiananmen suna ganin mutane iri-iri a kullum. A takaice, Gwamnatin kasar Sin tana bai wa wuraren tarihi da al'adu muhimmanci soasi, kuma yin haka din yana da kyau kwarai.

Alkalumar tarihi sun nuna mana cewar Taiwan wani yanki ne na kasar Sin. Amma saboda siyasar kasashen Yammaci (maras tushe) sai aka wayi gari wasu kasashe da 'yan kazaginsu masu son kai da kin gaskiya, suna "ingiza mai kantu ruwa" dangane da wannan muhimmin al'amari wajen tabbatar da Taiwan a kasar Sin.

Ko shakka babu, batun Taiwan magana ce mai girma. Taiwan za ta ci moriya masu dumbin yawa idan ba ta nemi ballewa ko warewa daga kasar Sin ba. Don kara tabbatar wa Taiwan da kuma Duniya baki daya wannan moriya, Shugaba Hu Jintao, a shekarar da ta gabata, ya gabatar da ra'ayoyi hudu a kan yalwata huldar da ke tsakanin bangarori biyu na zirin Taiwan na kasar Sin a cikin sabon hali.

Wadannan ra'ayoyi hudu sune:

"Za mu tsaya tsayin daka wajen bin ka'idar kasar Sin daya tak a Duniya; za mu yi iyakacin kokari wajen neman dinkuwar kasar Sin cikin lumana; ko da yaushe za mu sa ran alheri daga jama'ar Taiwan; kuma ko kiris ba za mu yi rangwame ga aikace-aikace da 'yan aware na Taiwan ke yi don neman ballewar Taiwan daga kasar Sin ba".

Saboda haka, a nawa ra'ayin, yanzu lokaci ya yi da Taiwan zata dauki matsayi guda wanda zai zama mata mataki mai tarin alheri da albarka da kuma amfani. Wannan mataki kuwa shi ne, na kasancewa tare da kasar Sin don cimma nasarorinta ba tare da tsangwama ba kamar yadda Macao da Hong Kong suka yi. "Daga kin gaskiya dai, sai bata".

A karshe, ina so mu sani cewar, kasar Sin tana da abubuwa masu yawa irin wadanda ba za su misaltu ko kirgu ba idan mutum zai yi rubutu ne a kai. Saboda haka, na yi kokarin yin wannan rubutu gwargwadon hali, don kuma a fahimce ni cewar kasar Sin kasa ce "son kowa kin wanda ya rasa".